Abba Gida Gida Ya Sauke Kwamishinansa, Ya Faɗi Dalili

Abba Gida Gida Ya Sauke Kwamishinansa, Ya Faɗi Dalili

  • Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sauke Alhaji Shehu Wada Sagagi daga mukaminsa nan take
  • Ya kuma umarci tsohon kwamishinan da ya miƙa ragamar aiki da dukkanin abubuwan da suka dace ga Daraktan kasuwanci
  • Gwamnatin Kano ta ce matakin wani ɓangare ne na sake fasalin gwamnati domin ci gaba mai ɗorewa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sallami Alhaji Shehu Wada Sagagi daga mukaminsa na Kwamishina.

Shehu Wada Sagagi shi ne kwamkshinan ma’aikatar zuba jari, kasuwanci da masana’antu, na jihar Kano gabanin a sauke shi, inda matakin ya fara aiki nan take.

Gwamnan Kano ya kori kwmishinansa daga bakin aiki
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf tare da Shehu Wada Sagagi Hoto: AbdulWahab Said Ahmad/Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Kano ya ga ta kansa, kotu ta shure rokon hana majalisa ta tsige shi

Abba ya kori kwamishina a Kano

A cewar sanarwar, an umarci tsohon kwamishinan da ya gaggauta miƙa dukkannin harkokin ma’aikatar ga daraktan kasuwanci domin ci gaba da tafiyar da ayyukan gwamnati ba tare da tangarda ba.

Gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki yana daga cikin sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi domin inganta tsarin tafiyar da mulki a jihar.

Duk da sauke shi daga mukami, Gwamna Yusuf ya yaba wa Sagagi bisa irin gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake kan kujera.

Ya ce tsohon kwamishinan ya taka rawar gani wajen bunƙasa harkokin siyasa da addini, tare da bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙananan da matsakaitan sana’o’i a jihar.

Fatan Abba ga tsohon kwamishinansa

Gwamnan ya kuma yi masa fatan alheri a rayuwarsa, yana mai fatan zai ci gaba da bayar da gudunmawa ga al’umma a wasu fannoni daban-daban.

Haka zalika, ya tabbatar wa al’ummar Kano cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da jajircewa wajen samar da ingantaccen aiki da kuma kyakkyawan shugabanci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fadi abin da ya hana Abba tarbar Sarki Sanusi a hawan Nasarawa

Gwamnan ya ce korar Sagagi na daga cikin tsarin sauya gwamnati
Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan mataki na daga cikin shirin sake fasalin tsarin gwamnati domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da ingantaccen tsarin gudanarwa.

Gwamnatin jihar ta jaddada cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakai masu muhimmanci da za su tabbatar da inganta ayyukan gwamnati da kuma biyan bukatun al’umma yadda ya kamata.

Wannan al'amari na zuwa ne a lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa tsakanin APC, NNPP da kuma ADC da ke kutso kai.

Kano: Mataimakin Abba ya gamu da cikas

A wani labarin, mun wallafa cewa Mataimakin gwamnan Kano Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo ya samu matsala a fafatawarsa da majalisar dokokin jiha.

A kwanakin baya, majalisar dokokin Kano ta sanar da shirin fara tsige Mataimakin gwamnan bisa wasu zarge-zarge da suka danganci almundahana da cin mutuncin ofis.

Wannan al'amarin ya tilasta wa Kwamred Aminu AbdulSalam Gwarzo garzaya wa kotu domin neman a taka wa majalisa birki, amma an samu koma baya baya a buƙatar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng