Ana Rade Radin Sheikh Khalifa Zariya Ya Rasu, Atiku Ya Yi Magana

Ana Rade Radin Sheikh Khalifa Zariya Ya Rasu, Atiku Ya Yi Magana

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi magana game da malamin Musulunci da aka kama, Sheikh Sani Khalifa Zariya
  • Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta bayyana malamin tare da kira a sake shi ko gurfanar da shi a gaban kotu
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da rade-radin cewa malamin ya rasu, inda wasu majiyoyi ke cewa yana nan da ran shi a tsare

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bukaci a gaggauta sakin wani malamin addini, Sheikh Sani Khalifa Zaria, ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.

Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan ci gaba da tsare malamin ba tare da an yi masa shari’a ba, inda ya ce hakan ya sabawa dokar kasa.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Kano ya ga ta kansa, kotu ta shure rokon hana majalisa ta tsige shi

Atiku Abubakar Sheikh Sani Khalifa Zariya
Sheikh Sani Khalifa Zariya a hagu, Atiku Abubakar a dama. Hoto: Sheikh Sani Khalifa Zariya/Paul O Ibe
Source: Facebook

Maganar Atiku kan Khalifa Zariya

Sanarwar da mai taimakawa Atiku kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya wallafa a Facebook ta ce an tsare Sheikh Khalifa ne bisa zargin hannu a shirin juyin mulki, amma har yanzu ba a gurfanar da shi a gaban kotu ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce wannan lamari ya saba kundin tsarin mulki da kuma dokar kare haƙƙin ɗan Adam, musamman ganin cewa wata kotun tarayya da ta umarci a gabatar da malamin a gabanta.

“Ba za a iya samun dimokuraɗiyya ba tare da cikakken bin doka ba. Babu wata hukuma ta tsaro da ta fi kundin tsarin mulki, kuma babu wadda ke da ikon ɗaukar haƙƙin ‘yan ƙasa a matsayin wani abu da zai juya yadda yake so,”

Inji sanarwar

Maganar kan tsare Sheikh Khalifa

Atiku ya yi gargadin cewa ci gaba da tsare malamin ba tare da damar ganin iyalansa, lauya ko samun kulawar lafiya mai kyau ba na nufin take haƙƙinsa na kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

'Abin ya yi yawa,' Fafaroma ya yi wa Trump da Iran wa'azi mai ratsa zuciya

Punch ta rahoto ya ƙara da cewa irin waɗannan matakai daga hukumomin tsaro na iya raunana dimokuraɗiyyar Najeriya tare da rage darajar haƙƙin ‘yan ƙasa.

Atiku ya nemi hukuma ta yi magana

Haka kuma ya nuna damuwa kan yadda ake ta jita-jita a cikin al’umma game da halin da malamin yake ciki, yana mai cewa yin shiru da hukumomi ke yi ya ƙara haifar da rashin tabbas da rashin amincewa.

Ya ce:

“Najeriya ba za ta iya ci gaba da kiran kanta ƙasa mai dimokuraɗiyya ba alhali ana yawan take haƙƙin ‘yan ƙasa a fili,”

Saboda haka, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bukaci hukumomin tsaron da abin ya shafa su saki Sheikh Khalifa nan take ko kuma su gurfanar da shi a gaban kotu ba tare da jinkiri ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
Atiku Abubakar yana wani jawabi a taro. Hoto: Atiku Abubakar
Source: UGC

Yaushe aka kama Sheikh Khalifa Zariya

A wani labarin, mun kawo muku cewa an tsare Sheikh Khalifa Zariya ne tun daga watan Disamban 2025 bayan kama shi a birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa tsare shi ya samo asali ne daga zargin tura kuɗi zuwa asusun bankinsa daga wani jami’in soja da ake dangantawa da yunkurin juyin mulki.

A watan Fabrairun 2026, an ruwaito cewa wata kotun da ke Abuja ta soki ci gaba da tsare malamin, amma har yanzu ba a gurfanar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng