El Rufa'i na Iya Samun Cikas, Kotu Ta Nuna Yatsa ga Neman Diyyar N1bn daga ICPC

El Rufa'i na Iya Samun Cikas, Kotu Ta Nuna Yatsa ga Neman Diyyar N1bn daga ICPC

  • LKotun tarayya ta soki shari’ar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya shigar gabanta game da ICPC
  • El-Rufa'i ya maka hukumar yaki da yi wa kasa ta'annati mai zaman kanta, ICPC a gaban kotu bisa zargin take masa hakki
  • Tsohon gwamnan ya ce an shiga gidansa ba bisa ka'ida, saboda haka ya nemi diyyar N1bn da keta masa alfarma da ya ce an yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Abuja – Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta nuna kura-kurai a cikin karar kare hakkin dan adam da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya shigar.

Karar, wacce aka kai a kan hukumar yaki da yi wa kasa ta'annati mai zaman kanta (ICPC) da wasu hukumomi guda hudu, ta fuskanci tangarda.

Kara karanta wannan

Makaman da Iran ta harba sun gigita Isra'ila, an ji barnar da suka yi

An samu kuskure a shigar da koken El-Rufa'i gaban kotu
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Business day ta wallafa cewa shari'ar ta samu tasgaro bayan ne bayan da aka gano cewa ba a bi wasu muhimman ka’idoji ba.

An gano kuskuren a karar El-Rufa'i

Jaridar Daily Nigerian ta wallafa cewa Mai shari’a, Joyce Abdulmalik, ta bayyana rashin gamsuwarta bayan gano cewa ba a cika ka'ida ba.

Lauyan El-Rufai Ugochukwu Nnakwu, ya shaida cewa bai iya isar da sammaci ga daya daga cikin wadanda ake kara ba, wato wani alkalin kotun majistare.

Lokacin da aka kira shari’ar, dukkannin bangarorin sun hallara a kotu, sai dai alkalin majistaren da aka saka a matsayin wanda ake kara na biyu bai halarta ba.

Lauyan ICPC, Isaac Akwo, ya bukaci a dakatar da zaman har zuwa 12.00 na rana domin babban lauyansa ya iso, amma kotu ta ki amincewa saboda wasu muhimman alƙawura da ke gabanta.

El-Rufa'i na ZARGIN ICPC ta take masa hakki
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i da ke shari'a da ICPC Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Facebook

Daga nan ne alkalin ta tambayi halin da ake ciki game da wanda bai halarta ba, inda lauyan El-Rufai ya amsa cewa har yanzu ba a kai masa sammaci ba, kuma ya nemi izinin yin hakan ta wata hanya ta daban.

Kara karanta wannan

Awanni da raka mahaifinsa kotu, Bello El-Rufai ya ziyarci babban dan siyasa a Kaduna

Sai dai alkalin ta katse shi tare da bayyana cewa dole ne ya fayyace sunan alkalin majistaren da ake magana a kai cikin takardun karar.

Wannan gyara ya sa lauyan El-Rufa'i ya amince da kuskuren tare da neman a dage shari’ar domin gyara.

Abubuwan da El-Rufai ke nema a kotu

Kotun ta amince da dage sauraron karar zuwa ranar 31 ga Maris 2026 domin sauraron bukatun da ke gaban kotu, tare da umartar a sake aika sammaci ga wanda bai karba ba. A cikin karar, El-Rufai na neman kotu ta yanke cewa samamen da jami’an ICPC tare da ‘yan sanda suka kai gidansa da ke Asokoro a ranar 19 ga Fabrairu, 2026 ya saba wa kundin tsarin mulki.

Ya bukaci kotu ta hana amfani da duk wata hujja da aka samu daga binciken, yana mai cewa an same su ne ta hanyar da ta saba doka, tare da neman a biya shi diyyar N1bn.

El-Rufa'i ya samu nasara

A baya, mun wallafa cewa kotun daukaka kara ta soke hukuncin kotun tarayya kan shari’ar da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya shigar.

Kara karanta wannan

Yadda matan El Rufai suka fuskanci turjiya wajen jami'an tsaro a kotu

Daga cikin dalilan da kotun ta bayar na soke hukuncin, ta ce ce an take masa hakkinsa na sauraron shari’a yadda ya kamata, saboda haka da sake

Ta bayyana mayar da shari’ar domin a sake sauraro a gaban wani alkalin daban yayin da El-Rufa'i ke hannun ICPC kan wasu zarge-zargen rashawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng