'Yan Kwangila Sun Shirya Jawo wa Babban Taron APC Tarnaki saboda Hakkokin Biliyoyoyi

'Yan Kwangila Sun Shirya Jawo wa Babban Taron APC Tarnaki saboda Hakkokin Biliyoyoyi

  • Ƙungiyar ƴan kwangila na cikin gida ta AICAN ta yi barazanar dirar mikiya a babban taron APC da aka shirya za a yi a Abuja
  • Ƴan kwangila sun bayyana takaici a kan yadda hakkokinsu ke neman shiga mawuyacin hali duk da sun kammala aiki lafiya lau
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa ƴaƴanta na neman a biya su Naira biliyan 150 a cikin awa 48 daga bashin ayyukan gwamnati da suka aiwatar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – Ƙungiyar ƴan kwangila a Najeriya (AICAN) ta bayyana cewa ƴaƴanta na iya gudanar da zanga-zanga a wurin taron ƙasa na jam’iyyar APC da za a yi a Abuja.

Ƙungiyar ta bayyana cewa za a tilasta mata daukan wannan mataki ne sakamakon jinkirin biyan kuɗin kwangilolin da suka yi wa gwamnatin Najeriya.

Kara karanta wannan

Pakistan za ta shiga tsakani a yakin Amurka da Isra'ila ke gwabzawa da Iran

Yan kwangila za su hargitsa taron APC
Shugaban Najeriya Bola Tinubu a ofis, Shugaban APC Yilwatda Nentawe a wani taro Hoto: Bayo Onanuga/Professor Yilwatda Nentawe
Source: Twitter

The Cable ta wallafa cewa Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Jackson Nwosu, ya bayyana haka ne a ranar Talata 24 ga watan Maris, 2026 yayin da ƴan ƙungiyar suka sake gudanar da wata zanga-zangar a Abuja.

Gwamnatin APC ta fusata ƴan kwangila

Peoples Gazette ta ruwaito cewa Nwosu ya ce ƙungiyar na neman a saki Naira biliyan 150 cikin sa’o’i 48 a matsayin wani ɓangare na kuɗin da aka amince a biya su kan ayyukan tarayya da aka tabbatar.

A cewarsa, gwamnati ta biya su Naira biliyan 21 kacal zuwa yanzu, duk da cewa bashin da ake binsu ya haura N1tr.

Ya ce:

“Gwamnati ta biya Naira biliyan 21 ne kawai a wannan lokaci. Abin da ya rage ya wuce N1tr, amma abin da muke nema yanzu shi ne a biya Naira biliyan 150 cikin gaggawa.”

Ya ƙara da cewa:

“Bukatar mu ita ce a biya wannan kuɗi tsakanin yanzu da cikin kwanaki biyu masu zuwa.”

Kara karanta wannan

Faransa za ta bi sahun Amurka, za a kawo wa Najeriya agaji a kan rashin tsaro

Ƴan kwangila za su ɗauki mataki

Ya yi gargadin cewa idan aka ci gaba da jinkiri, hakan zai sa su gudana da zanga-zanga a taron jam'iyyar APC na ƙasa domin fito da takaicin da ke damunsj.

A gefe guda kuma, Sakataren ƙungiyar na ƙasa, Seun Babatunde, ya ce yawancin ƴan kwangila na fuskantar matsin rayuwa sakamakon bashin da gwamnati ke hana

Ya bayyana cewa jinkirin biyan kuɗin ya shafi harkokin kasuwanci, biyan bashin banki, da kuma ci gaba da ayyukan da suke gudanarwa.

Yan kwangila za su kai kukansu taron APC tun da bin ofis ya ci tura
Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Yilwatda Nentawe Hoto: Professor Yilwatda Nentawe
Source: Twitter

Babatunde ya ce:

“Abin da AICAN ta samu zuwa yanzu shi ne Naira biliyan 21 daga cikin jerin biyan kuɗin da aka kammala a watan Disamba 2025.”

Ya kuma yi zargin cewa wasu daga cikin ƴan kungiyar sun rasa rayukansu saboda rashin samun kuɗin da su ke bi bayan sun shiga wani hali.

“Akwai wani ɗan ƙungiya da muka rasa sakamakon rashin lafiya, alhali yana bin gwamnati sama da Naira miliyan 100. Da an biya kuɗin, da an yi masa aiki."

Kara karanta wannan

"Yan ta'adda na amfani da bidiyon azabtarwa don firgita al’umma": Masani ya bayar da mafita

APC ta kwace iko da Majalisar dokoki

A baya, mun wallafa cewa Shugaban majalisar dokokin Zamfara da dukkannin sauran ƴan majalisa sun sauya sheka daga PDP zuwa APC domin bin sahun Gwamna Dauda Lawal.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya jagoranci taron karbar gwamna Dauda Lawal zuwa jam'iyyar APC a hukumance a ranar Talata 24 ga watan Maris na 2026.

Jam'iyyar APC mai mulki a ita ke da dukkanin kujeru 24 na majalisar dokokin jihar Zamfara bayan wannan gagarumin sauyin shekar da gwamnatin jihar ta jagoranta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng