Sunayen Manyan Jami'an 'Yan Sandan Najeriya da Suka Samu Sauyin Wuraren Aiki

Sunayen Manyan Jami'an 'Yan Sandan Najeriya da Suka Samu Sauyin Wuraren Aiki

  • Sufetun Janar na rundunar 'yan sanda ya tura manyan jami'ai zuwa sababbin wuraren aiki da suka hada da mataimakan sufeta janar da kwamishinoni
  • An nada sababbin kwamishinonin 'yan sanda a akalla jihohi takwas da kuma birnin tarayya Abuja domin karfafa shugabanci da magance rashin tsaro
  • IGP Olukayode Disu ya bukaci sababbin jami'an da aka tura su nuna kwarewa da kishin kasa wajen gudanar da sababbin ayyukansu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A wani babban mataki na ƙarfafa tsaro da inganta ayyukan rundunar ‘yan sandan Najeriya, Sufeton Janar (IGP) Olatunji Disu ya bada umarnin tura manyan jami’ai zuwa sababbin mukamai daban-daban a fadin kasar nan.

Wannan canji, wanda ya shafi mataimakan sufeta janar (AIGs) da kwamishinoni (CPs), an yi shi ne domin kara ingancin aiki, bunkasa karfin shugabanci, da kuma tabbatar da cewa dakarun ‘yan sanda suna bada kyakkyawar kariya ga rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa.

Kara karanta wannan

Matakin farko da alkali ya dauka a zaman shari'ar El Rufai da gwamnatin Najeriya

Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya ya yi sababbin sauye sauye a rundunar.
Wasu jami'an 'yan sanda da aka kara wa matsayi zuwa mataimakan sufeta janar da kwamishinoni a Abuja. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

An yi sauye-sauye a rundunar 'yan sanda

Kakakin rundunar ‘yan sandan kasa, DCP Anthony Okon Placid, ne ya sanar da wannan sabon tsarin tura jami’an a ranar Talata, a cewar rahoton Vanguard.

A cewarsa, wannan mataki yana tafiya ne daidai da burin rundunar na samar da tsari mai karfi a dukkan sassan gudanarwa, rundunoni, da kuma ofisoshin shiyyoyi na kasar nan.

Daga cikin manyan jami’an da aka tura akwai AIG Olohundare Moshood Jimoh, wanda yanzu zai jagoranci Shiyya ta 2 dake Legas, yayin da aka tura AIG Dahiru Mohammed zuwa Shiyya ta 15 a birnin Maiduguri.

Wasu daga cikin manyan jami’an da aka tura a hedkwatar rundunar dake Abuja sun hada da AIG Miller Dantawaye a sashen ayyuka, AIG Joseph Eribo a sashen makamai, da kuma AIG Ibrahim Balarabe Maikaba wanda zai jagoranci sashen shari’a.

Haka zalika, an tura AIG Bello Shehu zuwa Shiyya ta 14 dake Katsina, yayin da AIG Dankombo Morris zai koma Shiyya ta 4 dake Makurdi. Wadannan sauye-shiye sun nuna yadda rundunar ke kokarin tura jami’ai masu gogewa zuwa yankunan da ke fuskantar kalubalen tsaro daban-daban domin kawo karshen aikata laifuffuka.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da jami'an tsaro sun fafata ana shirin kama jagoran yan bindiga a Kano

Sababbin kwamishinoni da aka tura jihohi

Babban garambawul din ya kuma shafi kwamishinonin ‘yan sanda a jihohi da dama, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya nuna.

Daga cikin muhimman nade-naden akwai:

  • CP Olatunji Olaiwola Fatai - Jihar Legas.
  • CP Muhammed Sanusi Ahmed - Birnin Tarayya (FCT), Abuja.
  • CP Ahmed Mohammed Bello - Jihar Zamfara.
  • CP Haruna Alaba Yahaya - Jihar Jigawa.
  • CP Olugbenga Ayodeji Abimbola - Jihar Oyo.
  • CP Yemi John Oyeniyi - Jihar Delta.
  • CP Olubode Ojajuni - Jihar Ogun.
  • CP Umar Ali Fagge - Jihar Katsina.
  • CP Hayatu Shaffa Hassan - Jihar Sokoto.

Baya ga jihohi, an tura jami’ai zuwa sassa na musamman kamar CP Akan Ezima a matsayin daraktan yaki da laifuffukan intanet (NPF-NCCC), da kuma CP Ajo Geoffrey Ordue zuwa ofishin INTERPOL dake Abuja.

Har ila yau, an nada CP Rebecca Uchenna Okereke a matsayin Darektar kide-kide da wake wake a hedkwatar rundunar da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Sojoji sun yi dirar mikiya a sansanin Bello Turji, an yi kazamin artabu

Sabon sufeta janar ya yi garambawul a tsarin shugabancin rundunar 'yan sanda a fadin Najeriya.
Sufeta Janar na rundunar 'yan sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya na sanya lambar karin girma kan wani jami'i. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Sakon IGP ga 'yan sandan da sauyin ya shafa

IGP Olukayode Disu ya bukaci dukkan jami’an da wannan sauyi ya shafa da su yi amfani da tarin gogewar da suke da ita wajen gudanar da sababbin ayyukansu.

Ya jaddada cewa rundunar ba za ta amince da halin ko-in-kula yayin aiki ba, inda ya umarce su da su kiyaye ka’idojin aiki, horo, da kuma sanya kishin kasa a aikinsu.

A cewarsa, babbar manufar wannan canji shi ne ganin an samu sauki a matsalolin tsaro da suka addabi sassan Najeriya daban-daban ta hanyar amfani da sababbin dabarun shugabanci.

'Yan sanda 140 sun mutu saboda hawan jini

A wani labari, mun ruwaito cewa, Rundunar 'yan sanda a Abuja ta bayyana cewa ta rasa jami'ai 140 saboda hawan jini da ayyukan ta'addanci.

Rundunar ta ce wasu daga jami'an sun mutu ne suna tsaka da barci yayin da wasu suka mutu a bakin aiki.

Yayin da bayanai kan hakan suka fito, rundunar ta ce za ta kara mayar da hankali kan dabarun 'yan sanda, aikin leken asiri da wayar da kai ga jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com