Yarjejeniyar da Tinubu Ya Kulla da Turai Ana tsakiyar Yakin Amurka da Iran

Yarjejeniyar da Tinubu Ya Kulla da Turai Ana tsakiyar Yakin Amurka da Iran

  • Tarayyar Turai da Najeriya sun amince su hada gwiwa kan hakar ma'adanai da tsaro domin magance kalubalen tsaro da ke muni a duniya
  • Kaja Kallas. wakiliyar EU ta bayyana cewa Najeriya da Tarayyar Turai sun binciko sababbin hanyoyin hadin gwiwa da za su amfani kowane bangare
  • Wannan na zuwa ne yayin da Shugaba Bola Tinubu ya karbi tawagar Tarayyar Turai a gidansa dake Legas don karfafa kasuwanci da zuba jari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tarayyar Turai (EU) da ƙasar Najeriya sun cimma yarjejeniyar binciko hanyoyin haɗin gwiwa kan muhimman ma'adanai, zuba jari, tsaro, kasuwanci, da kuma tsaron intanet.

Wannan mataki ya zo ne yayin da ɓangarorin biyu ke neman ƙarfafa dangantaka a daidai lokacin da EU ta bayyana yanayin tsaron duniya a matsayin “mai matuƙar muni.”

Kara karanta wannan

Matakin farko da alkali ya dauka a zaman shari'ar El Rufai da gwamnatin Najeriya

Najeriya da Tarayyar Turai sun kara karfafa alaka ta bangarori 5
Shugaban kasa Bola Tinubu ya karbi bakuncin wakiliyar Tarayyar Turai a gidansa da ke Legas. Hoto: @kajakallas
Source: Twitter

Najeriya da Turai sun kulla yarjejeniya

Wakiliyar ƙungiyar EU kan harkokin waje da tsaro, Kaja Kallas, ita ce ta bayyana hakan a ranar Litinin bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu a gidansa dake Legas, in ji rahoton Punch.

Kallas, wadda ta gaji Josep Borrell a watan Disamba 2024, ta bayyana cewa:

“Mu abokan tarayya ne masu ra'ayi ɗaya, Tarayyar Turai da Najeriya. Kuma a yau mun binciko sababbin hanyoyin haɗin gwiwa.”

Wannan ganawa ta zo ne a daidai lokacin da ake fafatawa a duniya wajen neman ma'adanai irin su lithium, cobalt, da sauran abubuwan da ake amfani da su wajen kera batir na motoci, na'urorin hasken rana, da fasahar zamani.

Najeriya tana da tarin waɗannan ma'adanai, yayin da Tarayyar Turai ke ƙoƙarin rage dogaro da ƙasar China wajen samun su.

Turai za ta taimakawa Najeriya a fannin tsaro

Kaja Kallas ta jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin ƙasashe masu bin dokokin ƙasa da ƙasa, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Sojoji sun yi dirar mikiya a sansanin Bello Turji, an yi kazamin artabu

Ta ƙara da cewa sun tattauna da ministoci kan batutuwan zuba jari da kasuwanci, sannan akwai buƙatar ƙarfafa tsaron intanet fiye da yadda ake yi a baya.

"A irin wannan lokaci, akwai bukatar mu karfafa alakarmu, kama daga yaki da ta'addanci da kuma bangaren shige da fice don ganin an bunkasa kasuwanci da zuba jari."

- Kaja Kallas.

Najeriya ta ce a shirye take ta hada kai da Tarayyar Turai don bunkasa kasuwanci da tsaro
Ministoci da NSA, Ribadu na cikin ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da wakiliyar Tarayyar Turai. Hoto: @SundayDareSD
Source: Twitter

Tinubu ya ba Turai tabbacin shirin Najeriya

Shi ma mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya tabbatar da wannan zama, inda ya bayyana aniyar gwamnatin Tinubu na faɗaɗa wannan dangantaka, in ji rahoton jaridar Leadership.

Shugaba Tinubu ya tabbatar wa tawagar EU cewa Najeriya a shirye take ta ƙarfafa wannan kawance, sannan ya nuna godiyarsa kan goyon bayan da ƙungiyar ta riƙa ba Najeriya a baya.

Ganawar ta sami halartar Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Ministan Kasafi da Tsare-tsare, Sanata Abubakar Atiku Bagudu.

Ko da yake man fetur da iskar gas ne suka mamaye dangantakar kasuwanci tsakanin Najeriya da Turai a baya, wannan sabon mataki na nuni da sauya akala zuwa ga wasu fannonin tattalin arziki daban.

Kara karanta wannan

Faransa za ta bi sahun Amurka, za a kawo wa Najeriya agaji a kan rashin tsaro

Iran ta nuna sha'awar taimakawa Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Jakadan Iran a Najeriya, Gholamreza Mahdavi Raja, ya ce kasarsa a shirye take ta taimaka wa Najeriya wajen yaki da ta’addanci.

Gholamreza Mahdavi Raja ya bayyana goyon bayan Iran ga Najeriya kan barazanar Boko Haram da ISWAP, yana mai Allah wadai da ta’addanci a ko wane irin salo.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Iran din ke fafatawa da Amurka da Isra'ila a lokaci guda, a wani sabon yaki da ya kacame tun a karshen watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com