Yadda Matan El Rufai Suka Fuskanci Turjiya wajen Jami'an Tsaro a Kotu
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai a gaban kotu
- ICPC ta gurfanar da tsohon gwamnan ne a gaban babbar kotun tarayya da ke kaduna kan wasu tuhume-tuhume da take yi masa
- Yayin da ake gurfanar da tsohon gwamnan, wasu daga cikin matansa sun fuskanci turjiya daga wajen jami'an tsaro na hukumar DSS
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Daya daga cikin matan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, mai suna Asiya Ahmed El-Rufai, ta fuskanci turjiya wajen jami'an tsaro.
Jami'an tsaron na hukumar DSS sun hana matar El-Rufai shiga ta babbar ƙofar babbar kotun tarayya da ke Kaduna, inda hukumar ICPC ta gurfanar da mijinta a ranar Talata.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata, 24 ga watan Maris 2026 bayan da jami’an ICPC suka kawo tsohon gwamnan cikin zauren kotun da misalin ƙarfe 9:00 na safe.
An gurfanar da Nasir El-Rufai a kotu
Hukumar ICPC mai yaki da rashin gaskiya dai ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotun ne bayan ya kwashe kwanaki tsare a hannunta.
El-Rufai ya isa harabar kotun ne sanye da babbar riga bayan ya samu rakiyar jami'an tsaro masu yawa da kuma dinbin masoya a gefen kuliya.
Matan El-Rufai sun fuskanci turjiya
Asiya, wadda ta isa harabar kotun sanye da lulubi kalar toka, ta bayyana ta nuna bacin rai lokacin da ta yi ƙoƙarin shiga ta babbar ƙofar amma ta tarar da ita a kulle.
Ta tambayi wani jami’in tsaro na farin kaya (DSS) sanye da takunkumin fuska a bakin ƙofar da ya ba ta damar shiga, amma ya ƙi amincewa.
“Ni ce matar El-Rufai. Wa kake son na kira don a ba ni damar shiga?” ta tambaya, amma jami’in bai ce uffan ba.
Ta ƙara da cewa, “Abin da ke faruwa a nan yau zai wuce.”

Kara karanta wannan
Rana ba ta karya: Halin da ake ciki yayin da ICPC ta gurfanar da El Rufai a gaban kotu
Daga bisani aka ba ta umarnin ta bi ta ƙofar baya don shiga kotun, inda a ƙarshe ta bi ta can ɗin.
An bukaci matan su shiga ta kofar baya
’Yan mintuna kaɗan bayan nan, ita ma wata matar tsohon gwamnan, Khadija Ahmed El-Rufai, an hana ta shiga ta babbar kofar, inda jami’an tsaro suka buƙaci ta bi ta ƙofar baya.
Khadija, wadda take sanye da baƙar abaya da mayafi, ta nuna natsuwa yayin da take tafiya a cikin harabar don neman hanyar shiga zauren kotun.

Source: Twitter
Kotu ta dage zaman bukatar belin El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta yi matsaya kan bukatar neman beli da Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya gabatar.
Babbar kotun tarayyar ta ɗage sauraron buƙatar neman belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, zuwa ranar 31 ga watan Maris, 2026.
Hukumar yaƙi da cin hanci da hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (ICPC) ce dai ta gurfanar da El-Rufai tare da wani mutum mai suna Joel Adoga a gaban babbar kotun kan wasu tuhume-tuhume.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
