Yakin Amurka, Iran Na Cigaba da Taba 'Yan Najeriya, Farashin Man Fetur Ya Yi Tashin Gwauron Zabi
- Farashin da ake sayar da litar man fetur ya yi tashin gwauron zabi a babban birnin tarayya Abuja na Najeriya
- A wasu gidajen man fetur da ke birnin Abuja, farashin da ake sayar da litar man fetur ya fara jiyo kamshin N1,400
- Mutane da dama sun nuna korafinsu kan yadda farashin ya yi tashin gwauron zabi, inda suka nuna cewa akwai takura a cikin lamarin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Farashin man fetur a babban birnin tarayya Abuja na Najeriya ya yi tashin gwauron zabi.
A yanzu ana sayar da fetur a farashin N1,371 a kowace lita a wasu gidajen mai, lamarin da ya haddasa fushi a tsakanin masu amfani da man.

Source: Getty Images
Farashin man fetur ya tashi a Abuja
Binciken da jaridar Vanguard ta gudanar ya nuna cewa gidan man NIPCO yana sayarwa a kan N1,371 kan kowace lita.
Gidan mai na AYM Shafa yana sayarwa akan N1,370. Haka kuma, kamfanin NNPC Retail ya ƙara farashinsa zuwa N1,361 a kowace lita, daga N1,261 da yake sayarwa a makon da ya gabata.
Hakazalika gidan man MRS, wanda abokin hulda ne ga matatar Dangote, yanzu yake karɓar N1,367 kan kowace lita, daga N1,270 da yake sayarwa a baya.
Wannan karin ya biyo bayan sauye-sauyen farashin da matatar Dangote ta yi kwanan nan, wanda ya nuna kusan kashi 55 cikin 100 na ƙarin farashin fetur a cikin makonni uku da suka gabata.
Farashin fetur na ci gaba da tashi a Najeriya
Ƙarin farashin da aka yi a baya sun haɗa da:
- 3 ga Maris: NNPC a kan N975/lita, AYM Shafa akan N960/lita.
- 6 ga Maris: NNPC a kan N1,068/lita, AYM Shafa akan N1,098/lita.
- 9 ga Maris: NNPC ya tashi daga N1,161 zuwa N1,267/lita; AYM Shafa ya tashi daga N1,230 zuwa N1,300/lita.
An samu ɗan sauƙi na kwana biyu bayan nan, amma hakan bai ɗauki lokaci ba domin farashin ya sake yin sama a kwanakin da suka biyo baya.
Masu amfani da fetur sun nuna bacin ransu

Kara karanta wannan
Akwai kura: Dangote ya gano matsalolin da yakin Amurka, Iran zai jefa 'yan Najeriya
Yayin da suke magana a gidan man NNPC Retail da ke Kugbo da kuma AYM Shafa a Karu, mazauna yankin sun nuna damuwarsu kan yadda farashin man ke ƙaruwa, inda suka zargi gwamnatin tarayya da rashin ɗaukar mataki.

Source: Getty Images
Isa Kabir, wani ma’aikacin gwamnati, ya yi kira da a sanya idanu kan tsarin sayar da man, yana mai cewa:
“Cire tallafi bai kamata ya zama damar neman riba ba tare da kakkautawa ba. Daga N880 a farkon watan nan zuwa sama da N1,370 a cikin makonni uku kacal ya yi yawa. Idan babu wani tsari na tallafa wa jama’a, wannan zai tura ’yan Najeriya da dama cikin talauci.”
Wani ɗan tasi mai suna Michael Ade ya bayyana irin tasirin da hakan ke da shi a rayuwar yau da kullum, inda ya ce:
"Yanzu N10,000 tana sayen lita bakwai da ɗigo ne kawai na fetur, maimakon kusan lita 12 da take saya a watan da ya gabata. Kuɗin mota sun tashi daga N1,200 zuwa N2,000 ga tafiyar da aka saba yi, kuma zirga-zirga tana neman gagarar mutane da dama.”
Dangote ya kara farashin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar man Dangote ta kara farashin da take sayar da man fetur din da ta tace.

Kara karanta wannan
Yakin Amurka, Isra'ila da Iran ya taba Najeriya, farashin litar fetur ya haura N1350
Matatar ta hamshakin attajirin dan kasuwar ta sanar da abokan huldarta cewa ta ƙara farashin lita ɗaya daga ₦1,175 zuwa ₦1,245.
Hakazalika, matatar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon rikice-rikicen da ke ci gaba da faruwa a Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
