Tsadar Fetur: Gwamna Makinde Zai Rage wa Ma'aikata Wahala, Ya Ware Masu Alawus
- Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde ya amince da wasu kudi domin tallafa wa ma'aikatan jihar saboda tsadar man fetur
- Gwamnati ta bayyana cewa wannan matakin zai fara aiki na tsawon watanni uku domin rage wahalar rayuwa da jama'a suka shiga
- An dauki wannan mataki ne bayan tashin farashin man fetur a Najeriya wanda ya samo asali daga tsadar da mai ta yi a duniya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Oyo – Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya sanar da bayar da tallafin sufuri da za a rika ba wa ma'aikatan jihar duk wata.
Gwamnati ta sanar da cewa za a rika bayar da wannan tallafi na N10,000 na tsawon watanni uku domin rage wa ma'aikata radadi.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Makinde ya dauki wannan mataki ne sakamakon farashin man fetur da aka samu a baya-bayan nan.
Gwamna zai saukaka wa mutanen Oyo
Channels TV ta wallafa cewa Gwamna Seyi Makinde ya ce wannan tallafi zai fara aiki na tsawon watanni uku a matakin farko.
Ya ce an samar da tallafin domin rage radadin da ma’aikata ke fuskanta wajen biyan kudin zirga-zirga saboda tsadar fetur.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake duba yadda ake rabon tallafin shirin YEAP-SAFER tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a cibiyar Fashola Agribusiness Hub da ke Oyo.

Source: Facebook
Makinde ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na tunkarar matsin tattalin arziki, musamman yadda hauhawar kudin sufuri ke shafar aiki da jin dadin ma’aikata.
Ya kara da cewa gwamnati na da alhakin saukaka wa ma’aikata domin su ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba tare da tangarda ba.
Gwamnan Oyo ya tallata manufofinsa
Gwamnan ya jaddada cewa tallafin wani bangare ne na tsarin gwamnatin sa na tallafawa ma’aikata da kuma samar da saukin rayuwa karkashin shirin SAfER.
Ya ce gwamnati na sane da irin kalubalen da jama’a ke fuskanta, don haka tana daukar matakan da suka dace don rage musu radadi.
A yayin taron, an kuma raba kudi ga wadanda suka ci gajiyar shirin bunkasa harkokin noma na matasa (YEAP) da sauran shirye-shiryen tallafi da aka tsara domin farfado da tattalin arziki.
Masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun yabawa gwamnatin jihar bisa wannan mataki, inda suka ce an dauko aikin a lokaci ne da ya dace.
An bayyana cewa za a fara aiwatar da wannan tallafin daga watan Maris 2026, yayin da za a sanar da hanyoyin rabon kudin ta hanyoyin gwamnati da suka dace.
Gwamna Oyo na shirya magajinsa
A baya mun wallafa cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya ce yana iya zaɓar wanda zai gaje shi daga cikin jami'ansa yayin da aka fara shiri domin tunkarar zaben 2027.
Seyi Makinde ya bayyana cewa hakan zai tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan da gwamnatinsa ta fara shimfidawa wanda alummar jihar Oyo ke mora a yanzu.
Amma Gwamnan ya jaddada cewa duk da wannan shiri da ya ke yi talakawan jihar Oyo su ne ke da ta cewa a kan wanda zai ci gaba da jagorantarsu bayan wa'adinsa ya kare.
Asali: Legit.ng

