Ba Wasa: Sojoji Sun Yi Dirar Mikiya a Sansanin Bello Turji, an Yi Kazamin Artabu

Ba Wasa: Sojoji Sun Yi Dirar Mikiya a Sansanin Bello Turji, an Yi Kazamin Artabu

  • Dakarun sojojin Najeriya sun kai farmaki a sansanin tantirin jagoran 'yan bindiga, Bello Turji wanda ya dade yana addabar bayin Allah
  • Sojojin sun yi gumurzu da 'yan bindigan masu biyayya ga Bello Turji inda suka samu nasarar kashe da dama daga cikinsu
  • Wata majiya daga rundunar sojojin Najeriya ta bayyana yadda fafatawar ta kasance tsakanin jami'am tsaro da tsagerun 'yan bindiga masu kai hare-hare

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Dakarun sojojin Najeriya sun kashe hatsabiban ’yan bindiga da dama a sansanin Bello Turji.

Maɓoyar tasu tana yankin kauyen Fakai da ke ƙananan hukumomin Shinkafi da Isa a jihohin Zamfara da Sokoto.

Sojoji sun farmaki sansanin Bello Turji
Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaidu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce wata majiya a rundunar sojojin Najeriya wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar mata da kai harin a ranar Litinin, 23 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Da gaske 'yan bindiga 150 sun nutse cikin kogi a Sokoto? An ji gaskiyar zance

Sojoji sun yi artabu da 'yan bindiga

Majiyar ta bayyana cewa an samu wannan nasara ne yayin wani artabu da aka yi lokacin gudanar da samame na yau da kullum kan ayyukan ta’addanci a yankunan.

A cewar majiyar, samamen wanda rundunar ta musamman ta "8 Division Strike Force" ta sojojin Najeriya da ke Sokoto ta jagoranta, ya fara ne tun da sanyin safiyar ranar 20 ga Maris, inda aka nufi sansanin Turji da ke can cikin dajin Kagara.

Majiyar ta bayyana cewa yayin gudanar da samamen, wasu motocin yaƙi guda biyu sun sami matsalar inji kusa da ƙauyen Maberaya a ƙaramar hukumar Isa ta jihar Sokoto, wanda hakan ya tilasta wa dakarun dakatawa na ɗan lokaci.

Yaran Bello Turji sun yi wa sojoji kwanton bauna

Hakazalika majiyar ta ce a daidai wannan lokaci ne wasu gungun ’yan bindiga daga sansanin Bello Turji suka kai masu harin kwanton ɓauna.

“Sai dai dakarun sun mayar da martani cikin sauri da wuta mai ƙarfi, inda suka fafata da ’yan bindiga tare da kashe da dama daga cikinsu a gumurzun.”

Kara karanta wannan

Ana ruguntsumin Sallah, 'yan bindiga sun kai hari, an sace masu ibada

“Sojoji uku da jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ɗaya sun samu raunuka yayin artabun, kuma an kwashe su cikin gaggawa zuwa asibitin sojoji na 8 Division da ke Sokoto don yi musu magani."

- Wata majiya

Bello Turji da yaransa sun dade suna kai hare-haren ta'addanci a wasu yankunan jihohin Sokoto da Zamfara.

Sojoji sun yi artabu da yaran Bello Turji
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa Dakarun rundunar hadin gwiwa ta yankin Arewa maso Gabas, wato Operation Hadin Kai (OPHK), sun samu nasarar dakile wani hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai a sansanoninsu da ke Malam Fatori.

Sojoji sun samu nasarar fatattakar maharan tare da kashe akalla ‘yan ta’adda 80 a yayin fafatawar ta hanyar amfani da ingantacciyar hanyar sarrafa makami, hadin kai da kuma kwarewar dabarun yaki.

Farmakin ya yi sanadiyyar kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan ta’adda guda uku, wato Malam Abdulrahman Gobara, Malam Ba Yuram da Abou Ayyuba, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da jagorantar harin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng