Dara Ta Ci Gida: Ƴan Bindiga Fiye da 50 Sun Nutse yayin Tsallake Kogi a Sokoto

Dara Ta Ci Gida: Ƴan Bindiga Fiye da 50 Sun Nutse yayin Tsallake Kogi a Sokoto

  • Wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar yan bindiga a wani irin yanayi da ba a saba gani ba a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya
  • Rahotanni suka ce akalla ‘yan bindiga 150 sun nutse bayan jirgin ruwa da ke dauke da su ya kife a yankin Sabon Gida na Sokoto
  • Lamarin ya faru ne da yammacin Asabar 21 ga watan Maris, 2025 lokacin da jirgin ya kife yayin da yake ketare ruwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - A wani irin yanayi da ba a saba ganin irinsa ba, wasu yan bindiga sun mutu yayin da suke kokarin tsallake kogi a Sokoto.

An ce akalla maharan guda 150 ne suka mutu bayan wani jirgin ruwa da ke dauke da su ya kife a yankin Sabon Gida da ke Sokoto.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da yakin Iran da Isra'ila, jirgin sama ya yi hatsari, sojoji sun mutu

Yan bindiga 50 sun nutse a kogin Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da ke fama da hare-haren yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Majiyoyi daga yankin sun shaida wa Zagazola Makama cewa tabbas maharan sun mutu ne yayin ketare ruwan a jihar.

Bello Turji ya yi barazana ga yan Sokoto

Wannan na zuwa ne yayin da jihar Sokoto ke fama da hare-haren yan ta'adda kama daga sansanin Bello Turji da sauran hatsabiban miyagu.

Wasu mazauna wani yanki a jihar Sokoto suna cikin matsala mai muni bayan Bello Turji ya yi barazanar fatattakarsu.

Mazauna Bargaja a Sokoto sun fara tserewa daga gidajensu bayan barazanar kisa da hare-hare masu tsanani da suka dade suna faruwa.

Yan yankin suun koka da rashin tsaro, suna cewa hare-haren ‘yan bindiga sun zama ruwan dare, yayin da gwamnati ke kasa kawo karshensu.

Yan bindiga sun rasa rayukansu a Sokoto
Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Original

Yadda yan bindiga suka nutse a kogin Sokoto

An ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar 21 ga watan Maris sun shekarar 2026 lokacin da jirgin ya kife yayin ketare wani tafkin ruwa.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Sokoto bayan Turji ya yi barazanar tayar da kauye guda

An ce ‘yan bindigar suna tafiya ne cikin adadi mai yawa lokacin da jirgin ya juye kwatsam, inda ya jefa dukkan wadanda ke ciki cikin ruwa.

Wata majiya ta ce bayanan farko sun nuna cewa da dama daga cikinsu ba su iya iyo ba, lamarin da ya haddasa asarar rayuka mai yawa.

Wane martani hukumomin tsaro suka yi kan lamarin?

Rahotannin farko sun nuna cewa babu wanda ya tsira daga cikin wadanda ke cikin jirgin, duk da cewa babu tabbaci daga hukumomin tsaro.

Idan aka tabbatar da wannan lamari, ana sa ran zai zama babbar illa ga kungiyoyin masu aikata laifi da ke aiki a yankunan Arewa maso Yamma.

Yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Sokoto

Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai wani hari cikin dare karamar hukumar Rabah da ke fama da hare-hare a jihar Sokoto.

Bincike ya nuna cewa 'yan ta'addan da suka kai harin sun sace mutane wanda galibi mata ne, cikinsu akwai masu ciki da masu shayarwa.

Harin na zuwa ne bayan mahara sun kashe mutane suna sallah a wani masallaci a jihar Kebbi, inda ake cigaba da jimami a Najeriya kan harin yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.