Halin da Ake Ciki a Sokoto bayan Turji Ya Yi Barazanar Tayar da Kauye Guda
- Wasu mazauna wani yanki a jihar Sokoto suna cikin matsala mai muni bayan Bello Turji ya yi barazanar fatattakarsu
- Mazauna Bargaja a Sokoto sun fara tserewa daga gidajensu bayan barazanar kisa da hare-hare masu tsanani da suka dade suna faruwa
- Mazauna sun koka da rashin tsaro, suna cewa hare-haren ‘yan bindiga sun zama ruwan dare, yayin da gwamnati ke kasa kawo karshensu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Mazauna garin Bargaja da ke karamar hukumar Isa a Sokoto sun shiga cikin fargaba bayan Bello Turji ya umarce su da su bar garinsu ko kuma su fuskanci kisa.
Rahotanni sun nuna cewa daruruwan mata da yara sun tsere daga gidajensu, suna kokarin hawa mota dauke da kayansu domin tsira da rayukansu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.

Source: Original
Wani bidiyo da ya yadu da Vanguard ta samu ya nuna yadda mazauna ke cikin firgici, inda wasu mutane ke cewa sun dade suna kai masu hari suna kashe su.
Barazanar da Turji ya yi ga mazauna Sokoto
Sai dai rundunar sojoji ta ce ta shawo kan wasu mazauna su zauna, tana mai ba su tabbacin samar da tsaro a yankin.
Wasu majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 1:30 na dare, lamarin da ya jefa al’umma cikin tashin hankali da gudun hijira.
Wani masani kan tsaro ya ce ‘yan sa-kai sun yi artabu da maharan, amma an rasa rayukan mutane biyu daga cikinsu yayin musayar wuta.
An bayyana cewa hare-haren da ke da alaka da Bello Turji sun lalata rayuwar al’ummar yankin, inda aka kashe mutane da dama tare da tilasta wasu barin gidajensu.
A da Bargaja na daga cikin garuruwan noma masu arziki, amma yanzu gonaki sun zama kufai saboda tsoron hare-haren ‘yan bindiga.
Satar mutane da kuma satar dabbobi sun karu, lamarin da ya jefa iyalai cikin talauci tare da rasa hanyoyin samun abin dogaro.

Source: UGC
Yan Arewa sun fusata kan matsalar tsaro
Kungiyar 'Coalition of Northern Groups' ta yi Allah-wadai da lamarin, tana cewa matsalar tsaro na kara tabarbarewa a Arewacin Najeriya.
Shugaban kungiyar, Jamilu Aliyu Charanci ya ce lamarin Bargaja na nuna gazawar tsarin tsaro da kuma bukatar daukar matakin gaggawa.
Hakazalika, 'Arewa Defence League' ta bayyana cewa akwai gibi tsakanin manufofin gwamnati da ainihin tsaron da ke kasa, musamman a yankunan karkara.
Shugaban kungiyar, Murtala Abubakar ya ce dole ne gwamnati ta tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a domin dawo da kwanciyar hankali.
Yaran Bello Turji sun yi ta'asa a Sokoto
An ji cewa ’yan bindiga sun kai hari kauyen Kiratawa da ke Sabon Birni a Sokoto, inda suka kashe limamin gari a harin da ya girgiza al’umma.
Maharan sun kuma tare hanyar Takatsaba a gadar Dangulbi, inda suka yi kwanton-bauna suka harbe mutum guda har lahira.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin da ya tilasta mazauna kauyen tserewa a yankin da dauki dogon lokaci ba tare da kai hari ba.
Asali: Legit.ng

