Trump Ya Gaji da Jira, Ya ba Iran Wa’adin Awa 48 ko Ya Yi Mata Illa Mai Muni

Trump Ya Gaji da Jira, Ya ba Iran Wa’adin Awa 48 ko Ya Yi Mata Illa Mai Muni

  • Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar kai hari kan tashoshin wutar Iran yayin da ake ci gaba da yaki
  • Harin makamai masu linzami daga Iran ya jikkata mutane da dama a kudancin Isra'ila, yayin da ake shirin kara tsananta hare-hare a mako mai zuwa
  • Rikicin ya kara tsananta bayan harin Amurka da Isra’ila, inda Iran ta mayar da martani, lamarin da ya dagula harkokin mai da tattalin arzikin duniya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Wani sabon rikici ya sake daukar zafi tsakanin Amurka da Iran kan kulle mashigar ruwa ta Hormuz a yankin.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar kai hare-hare kan tashoshin wutar lantarki na Iran idan ba ta bude mashigar Hormuz cikin awa 48 ba.

Trump ya yi barazana ga Iran kan mashigar Hormuz
Shugaba Donald Trump na Amurka da mashigar Hormuz. Hoto: FADEL SENNA.
Source: Getty Images

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafin Trump na Truth Social wanda ya wallafa a jiya Asabar 21 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Amurka ta ji wuya: Trump ya cirewa Iran takunkumin man fetur

Hormuz: Barazanar da Trump ya yi ga Iran

Trump ya ce idan Iran ba ta bude mashigar ba, Amurka za ta lalata manyan cibiyoyin wutar lantarkin kasar, yana mai kara tsananta kalaman siyasa a rikicin.

A gefe guda, sojojin Isra'ila sun ce makamai masu linzami daga Iran sun afka birnin Dimona da Arad, inda suka jikkata mutane da dama tare da lalata gine-gine, bayan kariyar makamai ta kasa dakile wasu daga cikinsu.

Hukumomin agaji sun bayyana lamarin a matsayin babbar matsalar jikkata jama’a, inda akalla mutane 74 suka samu raunuka a hare-haren da suka faru a wurare daban-daban.

Haka kuma, Birtaniya ta zargi Iran da kai hari marasa hankali bayan an harba makamai zuwa sansanin hadin gwiwa na Amurka da Birtaniya da ke Diego Garcia, kodayake ba su kai ga kai hari kai tsaye ba.

Trump ya ba Iran wa'adin awa 48 ko ya kai mata hari
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Yadda Iran ta harba makamai masu dogon zango

Rahotanni sun nuna cewa Iran ta harba makamai masu linzami masu matsakaicin zango, wanda ya haifar da damuwa kan iyakar karfin hare-harenta fiye da yadda aka sani a baya.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta jawo wa kanta, Rasha ta shiga kafar wando daya da ita kan hari a Lebanon

A lokaci guda, rundunar sojojin Isra'ila sun ce za su kara tsananta hare-hare kan Iran a wannan mako, duk da cewa Trump ya taba nuna yiwuwar rage yaki a baya.

Rikicin ya samo asali ne tun bayan hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a ranar 28 ga Fabrairun 2026, wanda ya janyo martanin Iran da harba makamai da jiragen yaki marasa matuki zuwa kasashen yankin.

Sakamakon haka, mashigar Hormuz ta kusa rufewa, lamarin da ya haifar da tashin farashin mai a duniya da kuma matsin tattalin arziki a kasashe da dama.

Masana sun ce wannan rikici na iya kara tsananta idan ba a samu mafita ta diflomasiyya ba, musamman ganin yadda bangarorin ke ci gaba da nuna karfin iko da mayar da martani da karfi.

Kasashe 5 sun yi fatali da bukatar Trump

An ji cewa Shugaba Donald Trump ya bukaci kasashe biyar su tura jiragen yaki zuwa mashigar Hormuz amma har yanzu babu wanda ya amince.

Japan da Faransa sun nuna rashin amincewa da bukatar, yayin da Birtaniya ke tattaunawa da kawaye.

Ana fargabar Iran ta dasa nakiyoyi a mashigin ruwan da ke da muhimmanci ga safarar man fetur ta duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.