"An San Masu Ɗaukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya," Tukur Buratai Ya Yi Bayani

"An San Masu Ɗaukar Nauyin Ta'addanci a Najeriya," Tukur Buratai Ya Yi Bayani

  • Tukur Buratai ya bayyana cewa an san masu daukar nauyin ta'addanci a Najeriya kuma suna cikin al'umma, amma hukumomi suna da dalilin boye sunayensu
  • Janar din ya kuma yi tsokaci kan shirin gyaran tarbiyar tubabbun 'yan ta'addan Boko Haram, yayin da ya bukaci a dauki karin jami'an tsaro a Najeriya
  • Al'ummar Najeriya na ci gaba da matsa lamba ga gwamnati tun shekarar 2021 domin a bayyana sunayen masu tallafa wa ayyukan ta'addanci a kasar nan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsohon shugaban rundunar sojin kasa, Tukur Buratai, ya bayyana cewa kada a ɗora masa alhakin rashin bayyana sunayen mutanen da ake zargi da daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Buratai ya jaddada cewa waɗannan mutane sanannu ne kuma suna nan a raye cikin al'umma, amma hukumomin da abin ya shafa suna da dalilansu na rashin bayyana sunayensu ga jama'a.

Kara karanta wannan

Ana shagulgulan Sallah, ƴan ta'adda sun sace jami'in gwamnatin jihar Kano

Tukur Yusuf Buratai ya ce an san wadanda ke daukar nauyin ta'addanci a Najeriya.
Tsohon babban hafsan sojojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai. Hoto: Tukur Buratai
Source: Facebook

"An san masu daukar nauyin ta'addanci'

Da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels a jiya Juma'a, Janar Buratai ya bayyana cewa:

"Ba za ku ce ni ne ya kamata in ɗauki alhakin bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci ba. Hukumomin da abin ya shafa sun san dalilin da ya sa ba a bayyana sunayen ba.
"Ya kamata a ɗauki mataki; waɗannan mutane suna nan cikin al'umma a yau, kuma an san su."

Ya ƙara da cewa shi yana ɗaukar alhakin abubuwan da suka shafi ayyukan rundunar sojin ƙasa ne kawai kai-tsaye, ban da wadanda suka shafin sauran hukumomin.

Matsayar Buratar kantubabbun 'yan Boko Haram

Buratai ya kuma yi ƙarin haske kan takaddamar da ake yi game da shirin gwamnati na gyaran tarbiyar tubabbun 'yan kungiyar Boko Haram tare da mayar da su cikin al'umma.

Ya bayyana cewa wannan shawara ce ta gwamnati ba wai ta soja ba. A cewarsa, shirin da sojoji suka yi tun farko a shekarar 2016 shi ne ba 'yan ta'addan wa'adin mika wuya, sannan a mika su ga hukumomin da suka dace domin gyara halinsu.

Kara karanta wannan

Iran ta yi babban rashi a ranar Sallah, kakakin rundunar IRGC ya mutu a harin Isra'ila

Bugu da ƙari, tsohon jakadan ya nuna damuwarsa kan ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta, inda ya yi kira da a ƙarfafa tattara bayanan sirri domin yaƙar ta'addanci. Ya kuma buƙaci gwamnati da ta ɗauki ƙarin jami'an tsaro domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi a faɗin ƙasar.

Janar Tukur Buratai ya ce ba shi ne yake da alhakin fadin sunayen masu daukar nauyin ta'addanci ba.
Tsohon babban hafsan sojojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai. Hoto: Tukur Buratai
Source: Facebook

Bukatar sanin masu daukar nauyin ta'addanci

An dade ana kira ga gwamnatin tarayya da ta bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci, kuma har yanzu ana ci gaba da yi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tun a shekarar 2021, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta gano wasu mutane da kungiyoyi da ke tallafa wa ta'addanci, lamarin da ya sa jama'a ke sa ran jin sunayensu.

Hukumar lura da hada-hadar kuɗaɗe ta ƙasa (NFIU) ta taɓa nuna cewa ta gano wasu hanyoyin hada hadar kuɗaɗe da ke da alaƙa da ta'addanci, amma har yanzu ba a bayyana sunayen ba.

Sunayen masu daukar nauyin ta'addanci

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Najeriya ta ayyana Simon Ekpa, kungiyar Lakurawa da wasu mutum 14 a matsayin masu daukar nauyin ta’addanci.

An bukaci bankuna da cibiyoyin kasuwanci su toshe duk wasu kudi ko kadarori da ke da alaka da mutanen da aka bayyana a jerin.

Sunayen da aka fitar sun hada da Ekpa, Godstime Promise Iyare, da wasu kamfanoni kamar Igwe Ka Ala Enterprises da Seficuvi Global.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com