Kwana Ya Kare: Hadimin Gwamna Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu a Wurin Taro

Kwana Ya Kare: Hadimin Gwamna Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu a Wurin Taro

  • An tabbatar da mutuwar babban mai tsara ayyukan gwamnan jihar Delta, Sunday Kotor bayan ya yanke jiki ya fadi a wurin taro
  • Gwamna Sheriff Oborevwori ya yi alhinin rasuwar Sunday Kotor tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalai da sauran 'yan uwansa
  • Rahoto ya nuna cewa marigayin ya fadi ne a wani taro da ya shirya na kashin kasa, likitoci suka tabbatar da ya mutu bayan an garzaya asibiti

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya nuna matukar alhini kan rasuwar Mai Taimaka Masa na Musamman kan harkokin tsare-tsare, Sunday Kotor.

Gwamnan ya bayyana rasuwar tasa a matsayin babban rashi ga gwamnati da al’ummar jihar Delta baki daya.

Gwamnan Delta.
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori a fadar gwamnatinsa Hoto: Rt. Hon. Sheriff Oborevwori
Source: Facebook

Hadimin gwamnan Delta ya rasu

Rahoton The Nation ya nuna cewa Kotor ya rasu ne bayan ya fadi a wani taro na kashin kai da aka gudanar a yammacin ranar Juma’a, 20 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Ali Larijani: Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei ya dauki zafi, ya tura sako ga Amurka da Isra'ila

An garzaya da shi zuwa asibiti nan take domin ceto rayuwarsa, amma duk kokarin likitoci bai yi nasara ba, inda daga bisani aka tabbatar da cewa rai ya yi halinsa.

A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Sir Festus Ahon, ya fitar, Oborevwori ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen ma’aikacin gwamnati mai kishin aiki.

Ya ce:

“Marigayi Sunday Kotor ya kasance mai sadaukarwa ga aikinsa. Rasuwarsa babban rashi ne ba ga iyalinsa kadai ba, har ma ga gwamnati da al’ummar jihar Delta.”

Gwamna ya yi ta’aziyya ga iyalai

Gwamnan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, musamman kaninsa Conference Kotor, wanda shi ma ke aiki a matsayin mai taimaka masa kan harkokin yada labarai.

Oborevwori ya ce gudunmawar da Kotor ya bayar wajen tsara taruka da ayyukan gwamnati za ta dade ana tunawa da ita, kamar yadda TVC News ta ruwaito.

Takaitaccen bayani kan Sunday Kotor

Marigayin ya kasance fitacce a gidan gwamnati da ke Asaba, inda ya shafe sama da shekaru 20 yana jagorantar manyan bukukuwa da tarukan gwamnati a matsayin mai gabatar da shirye-shirye.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

Kotor ya yi aiki a karkashin gwamnatocin da suka gabata ciki har da na tsofaffin gwamnoni Emmanuel Uduaghan da Ifeanyi Okowa, sannan ya ci gaba da aikinsa a gwamnatin yanzu.

Sunday Kotor.
Maeigayi hadimin gwamnan jihar Delta, Sunday Kotor Hoto: Sunday Kotor
Source: Facebook

Ya kammala karatunsa a fannin aikin jarida a Jami’ar Jihar Delta da ke Abraka, kuma ya fito ne daga garin Okwagbe a masarautar Ughievwen, karamar hukumar Ughelli ta Kudu.

Tsohon mataimakin gwamnan Delta ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin gwamna a jihar Delta, Chif Benjamin Elue ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 85 a duniya.

Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tsohon mataimakin gwamnan, yan mai bayyana shi a matsayin mutumin kirki.

Gwamnan ya ce ya samu labarin rasuwar cikin kaduwa da radadi, amma tare da godiya ga Allah kan rayuwa mai cike da hidima da marigayin ya yi wa Delta da Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262