Ana Shagulgulan Sallah, Ƴan Ta'adda Sun Sace Jami'in Gwamnatin Jihar Kano
- Wasu ƴan ta'adda aƙalla shida sun sace sakataren mulki na Karamar Hukumar Kibiya, Hon. Hamza Musa Durba
- Maharan sun kutsa kauyen a kan babura dauke da bindigu a daren Asabar inda suka shugabar gidan jami'in gwamnatin
- Rahotanni sun sace duk da an sanar da jami'an tsaro, ƴan ta'addan sun yi gaggawar kammala abin da ya kai su
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – ’Yan ta'adda sun sace sakataren mulki na Karamar Hukumar Kibiya da ke jihar Kano, Hon. Hamza Musa Durba, a daren Asabar 20 ga watan Maris 2026.
Wannan al'amari ya jefa al’umma cikin fargaba da zaman dar-dar, yayin da miyagun mutanen suka shiga garin da manyan makamai.

Source: Original
Arewa Updates ta wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a gidansa da ke garin Dinya, a mazabar Durba, inda suka yi awon gaba da shi ba.

Kara karanta wannan
Iran ta yi babban rashi a ranar Sallah, kakakin rundunar IRGC ya mutu a harin Isra'ila
Yadda ƴan ta'adda suka shiga Kibiya
Rahoton ya ce babban jami’in harkokin tsaro na karamar hukumar Kibiya, Malam Musa Hussaini Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sanar da jami'an tsaro.
A cewarsa, maharan su shida ne, kuma sun isa garin a kan babura dauke da bindigu, inda suka shiga gidan sakataren cikin dare ba tare da sun fuskanci tirjiya ba.
Ya bayyana cewa lokacin da suka shiga gidan, sun tarar da iyalansa amma ba su dauki kowa ba, kuma ba su harba bindiga ba.
A cewarsa:
“Sun zo kai tsaye suka dauke shi, ba tare da sun yi wani tashin hankali ba. Sun sa shi a gaba suka tafi da shi.”
Jama'a sun farga da harin ƴan ta'adda
Malam Musa Hussaini ya kara da cewa wasu mazauna yankin ne suka fara lura da abin da ke faruwa, inda suka sanar da dagacin garin.
“Mutanen gari ne suka ga motsin, suka sanar da dagaci, shi kuma ya sanar da ni. Ni kuma na sanar da jami’an tsaro nan take."

Source: Twitter
Sai dai kafin jami’an tsaro su iso wurin, maharan sun riga sun tsere da wanda suka sace tare da barin iyalansa a cikin tashin hankali.
Bayan faruwar wannan lamari, hukumomin tsaro sun fara gudanar da bincike tare da bin sahun maharan domin ganin an ceto sakataren cikin koshin lafiya.
Majiyoyi sun ce ana kokarin gano inda maharan suka nufa, tare da kara tsaurara matakan tsaro a yankunan da ke kewaye da karamar hukumar.
Har yanzu ba a fitar da wata sanarwa kan ko an tuntubi iyalan wanda aka sace domin neman kudin fansa ba.
Dalilin dawowar ta'addanci da ƙarfi - Tinubu
A baya, mun wallafa cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana game da hare-haren 'yan kunar bakin wake da aka kai birnin Maiduguri na jihar Borno.
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa hare-haren sun shafi wurare uku kuma sun jawo mutuwar jama'a da dama da jikkata wasu da dama da ke asibiti yanzu.
Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da daukar matakan da suka dace domin magance barazanar 'yan ta'adda a dukkanin sassan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
