An Samu Matsala: Dangote Ya Ƙara Kuɗin Fetur, Lita Ta Haura N1240

An Samu Matsala: Dangote Ya Ƙara Kuɗin Fetur, Lita Ta Haura N1240

  • Matatar man Dangote ta kara farashin man fetur da take sayarwa abokan huldarta da ₦70, wanda ke nufin lita daya yanzu ta koma ₦1245
  • Sabon farashin zai fara aiki ne daga karfe 12:00 na daren yau Asabar, kuma zai shafi har da man da aka biya kudinsa amma ba a dauka ba
  • An dora alhakin wannan karin kudin a kan tashin hankalin da ake fama da shi a Gabas ta Tsakiya wanda ya shafi farashin danyen mai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Legas - Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da abokan cinikinta cewa ta sauya farashin man fetur (PMS), inda aka samu ƙarin kuɗi yanzu.

A sakon da matatar ta aike wa abokan hulɗarta, ta sanar da su cewa ta ƙara farashin lita ɗaya daga ₦1,175 zuwa ₦1,245.

Kara karanta wannan

Rabon shinkafar Tinubu: Yadda ake 'bambance' Kudu da Arewa wajen tallafa wa mutane

Matatar man Dangote ta kara farashin litar man fetur da N70.
Hagu zuwa dama: Alhaji Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, da wani ma'aikaci yana sayar da fetur. Hoto: Dangote Industries|Getty Images
Source: Getty Images

Dangote ya ƙara kuɗin man fetur

Wannan na nufin an samu ƙarin ₦70 a kan kowace lita ɗaya ta man fetur ɗin da ake saya daga matatar, kamar yadda Imran Muhammad ya wallafa a shafinsa na X.

Matatar Dangote ta ce wannan sabon farashi zai fara aiki ne daga ƙarfe 12:00 na daren yau, watau wayewar garin Asabar, 21 ga Maris, 2026.

Haka zalika, wannan ƙarin zai shafi dukkan man da aka riga aka biya kuɗinsa amma ba a ɗiba ba tukuna daga matatar.

Dalilin ƙarin kuɗin man fetur

Baya ga ƙarin farashin lita, matatar ta kuma ƙara farashin samar da man ta hanyar ruwa daga ₦1,512,648 zuwa ₦1,606,518 a kan kowane tan ɗaya.

Matatar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon rikice-rikicen da ke ci gaba da faruwa a Gabas ta Tsakiya, wanda ya shafi harkar makamashi gaba ɗaya.

Matatar Dangote ta kara farashin man fetur
Matatar Dangote ta kafa wa 'yan kasuwa sharadi yayin da ta kara kudin man fetur. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Sharudan sayen fetur din Dangote

Kara karanta wannan

"Yan ta'adda na amfani da bidiyon azabtarwa don firgita al’umma": Masani ya bayar da mafita

Matatar ta fayyace cewa abokan huldarta da ke da Bank Guarantees a turance, za su iya ci gaba da loda man su a ƙarƙashin tsarin da suke kai, muddin sun amince za su biya sauran ragowar kuɗin da aka ƙara a kai.

Hazalika, dole ne duk wani mai sayen mai da ake binsa ragowar kuɗin wannan ƙarin, ya kammala biya kafin ranar Litinin, 23 ga Maris, 2026, kamar yadda rahoton shafin Pulse ya nuna.

Wannan ƙarin na zuwa ne a daidai lokacin da farashin danyen mai ke ci gaba da tashi a kasuwannin duniya sakamakon rikicin da ake fafatawa a Gabas Ta Tsakiya tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila.

Tsadar sufuri a Najeriya saboda tsadar mai

Yayin da litar man fetur ta kai har N1,330 a wasu gidajen mai a Najeriya, Legit Hausa ta fahimci cewa an samu tsadar abun hawa a jihar Kaduna da kewaye.

A jihar Kaduna, masu adaidaita sahu da ke zirga-zirga daga cikin Dan Mani, Rigasa, zuwa Kasuwar Bacci da Kawo, sun kara kudin sufuri daga makon jiya.

Amina Lawal Mailafiya da ta saba hawa keke-napep daga Poll Wire zuwa bakin titin shiga Dan Mani a kan N150, ta ce kudin ya karu zuwa N250.

Kara karanta wannan

Bukukuwan Sallah: Jerin gwamnonin Arewa 5 da za su biya albashin Maris da wuri

"Na shiga keke kamar yadda na saba, sai da muka sauka, na ciro N150 na mika, aka ce mun sai na ciko N100, wai an kara kudi saboda litar fetur ta koma ko N1330, na dai manta nawa suka ce.
"Sannan daga bakin titi zuwa Kasuwar Bacci muna biyan N250 ko N300, amma aka ce mun an kara kudin zuwa N400."

- Amina Lawal Mailafia.

Yaki da Iran ya kara taba Dangote

A wani labari, mun ruwaito cewa, a karo na uku cikin mako guda, matatar Dangote ta kara farashin litar man fetur a wuraren da take ba yan kasuwa sari a Najeriya.

Wannan kari da ake yawan samu a bayan bayan nan na da nasaba da yakin Iran da Amurka/Isra'ila, wanda ya jawo tashin danyen mai a duniya.

Kungiyar PETROAN ta yi hasashen cewa idan ba a dakatar da wannan yaki ba, farashin fetur zai iya kai wa N2,000 a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com