Yaki Ya Yi Ƙamari, Amurka Za Ta Sayar da Makaman Biliyoyi ga Makwabtan Iran
- Kasar Amurka ta amince da yarjejeniyar sayar da makamai na dala biliyan 16.5 ga kasashe makwabtan Iran
- Hakan ya biyo bayan ci gaba da yaki da ake yi tsakanin Iran da kasar Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka
- Kasashen da Amurka ta kulla yarjejeniyar da su sun hada Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait da Jordan yayin da rikici da Iran ke kara tsananta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da yarjejeniyar sayar da makamai ta $16.5bn ga kasashen Larabawa.
Kasashen sun hada da Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait da Jordan yayin da rikici da Iran ke kara tsananta.

Source: Facebook
Makaman da Amurka za ta sayar wa Larabawa
Ma’aikatar ta bayyana cewa za a bai wa Hadaddiyar Daular Larabawa makamai na kusan dala biliyan 8.4 da suka hada da jiragen yaki, makamai masu linzami da na’urorin radar, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan
Kasashe 5 da suka kira Iran ta waya, suka nuna ana tare bayan fara yaki da Amurka
Haka kuma, Amurka ta amince da kusan $8bn domin samar da tsarin kariya daga hare-haren sama da makamai masu linzami ga Kuwait, tare da karin $70.5bn ga Jordan.
Ma’aikatar ta ce wannan yarjejeniya za ta taimaka wajen cimma manufofin tsaro da siyasar ketare na Amurka, tare da karfafa manyan abokan huldarta a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ta kuma kara da cewa ba sai Majalisar Dokoki ta amince ba, domin minista Marco Rubio ya bayar da hujjar gaggawa da ke bukatar sayar da makaman nan take
Yarjejeniyar ta zo ne yayin da rikici tsakanin Amurka da Iran ke kara kamari, bayan hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran tun ranar 28 ga Fabrairun 2026.
Yakin ya janyo fargabar barkewar rikici mai tsawo a yankin, tare da haddasa tashin farashin makamashi a duniya sakamakon hare-haren kan cibiyoyin mai.
Iran ta mayar da martani da barazanar kai hari kan cibiyoyin makamashi na kawayen Amurka kamar Qatar da Saudiyya, lamarin da ke kara dagula yanayin tsaro.

Source: Twitter
Kamfanonin da za su samar da makaman
Kamfanonin da za su samar da makaman sun hada da RTX, Northrop Grumman da Lockheed Martin, duk da cewa hannayen jarinsu suna faduwa a kasuwar 'Wall Street'.
A lokaci guda, ma’aikatar tsaron Amurka na neman karin kudade har $200bn domin tallafawa yakin, duk da cewa hakan na bukatar amincewar Majalisa.
Sakataren tsaro Pete Hegseth ya ce ana bukatar karin kudade sosai, yana mai jaddada cewa yaki na bukatar kudi domin cimma nasara, cewar TRT World.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kare bukatar karin kudaden, yana cewa duniya na cikin yanayi mai hadari wanda ke bukatar karin shiri da tsaro.
Iran ta kai hari ana tsaka da taro
An ji cewa a ranar Laraba, 18 ga watan Maris 2026 shugabannin kasashen Musulmi da Larabawa suka gudanar da taron gaggawa kan yakin Iran.
Yayin da suke tsaka da taron, an ji saukar makaman Iran a birnin Riyadh, lamarin da ya jawo tashin hankali da martani daga mahalarta.
Tun karshen watan Fabrairun 2026 Amurka da Isra'ila suka kaddamar a hari a kan Iran, lamarin da ke cigaba da shafar kasashen Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng
