Kiristoci Sun Fusata da Kalaman Netanyahu kan Zargin Taba Mutuncin Annabi Isa

Kiristoci Sun Fusata da Kalaman Netanyahu kan Zargin Taba Mutuncin Annabi Isa

  • Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya jawo ce-ce-ku-ce bayan kalamansa kan Annabi Isa (AS) da Genghis Khan
  • Jama’a sun caccaki kalamansa a shafukan sada zumunta, suna zargin sa da nuna ƙiyayya ga Kiristoci
  • Netanyahu ya musanta zargin, yana cewa bai taba raina Annabi Isa ba kuma Kiristoci na samun kariya a Isra’ila

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Firayim ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi ƙarin haske game da zargin taba mutuncin Annabi Isa a kasar Isra'ila.

Netanyahu ya jawo ce-ce-ku-ce ne bayan wata magana da ya yi a taron manema labarai da ta shafi Annabi Isa (AS).

Netanyahu ya kare kansa kan zargin taba kimar Annabi Isa
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Abir Sultaan.
Source: Getty Images

Zargin da Kiristoci ke yi wa Netanyahu

Rahoton Financial Express ya ce Netanyahu ya jawo magana ne yayin jawabinsa inda aka ce ya hada tasirin Annabi Isa da Genghis Khan.

Kara karanta wannan

Yadda Isra'ila ta amsa bukatar Trump, Netanyahu ya magantu kan kawo karshen yaki

A jawabinsa, an ce Netanyahu ya ce Annabi Isa ba shi da wata fa'ida fiye da Khan inda ya ce idan mutum ya kasance mai karfi da rashin tausayi to mugunta za ta yi tasiri.

A cikin jawabin nasa, Netanyahu ya ce:

"Annabi Isa ba shi da wata fa’ida fiye da Genghis Khan. Idan mutum ya kasance mai ƙarfi da rashin tausayi, sharri zai rinjayi alheri.”

Wannan magana ta jawo martani mai zafi daga jama’a musamman al'ummar Kiristoci wadanda suka ganin ya ci mutuncinsu.

Cikin sa’o’i kaɗan, bidiyon ya bazu a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama suka bayyana kalaman a matsayin abin takaici, suna zargin sa da nuna adawa da Kiristoci, wasu sun ce wannan na nuna ainihin ra’ayinsa game da addinin Kirista.

An caccaki Netanyahu kan taba Kiristoci a Isra'ila
Firayim ministan Isra'ila da ke yaki da Iran, Benjamin Neyanyahu. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Getty Images

Martanin Netanyahu kan zargin taba Kiristoci

Sai dai Netanyahu ya musanta wannan zargi, yana mai cewa ana yaɗa ƙarya game da matsayinsa kan Kiristoci.

Ya jaddada hakan a wani rubutu a shafinsa na X a jiya 19 ga watan Maris, shekarar 2026 da muke ciki inda ya ce Kiristoci na samun kariya kuma suna bunƙasa a Isra’ila.

Kara karanta wannan

Trump ya yi magana da babban jigo a tsaron Amurka ya yi murabus saboda yaki da Iran

“Bari in fayyace, ban raina Annabi Isa ba a jawabin da na yi."

A gefe guda, Netanyahu ya sake bayyana cewa Isra’ila ce kaɗai ta kai harin kan filin gas na Pars a Iran, yana mai cewa daga baya shugaban Amurka Donald Trump ya roƙe su su dakatar da ƙarin hare-hare.

Netanyahu ya kare Trump kan yaki da Iran

Mun ba ku labarin cewa Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana kan tsoma Amurka cikin yakin da suke yi da Iran.

Netanyahu ya ce Isra’ila ta kai hari kan Iran ita kaɗai ba tare da sa hannun Amurka ba a yaƙin zai ƙare da wuri fiye da yadda ake tsammani

Firayim ministan ya kare Amurka da shugabanta, Donald Trump inda ya musanta cewa Isra’ila ce ta jawo Amurka cikin yaƙin, yana mai cewa zargin hakan ba shi da tushe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.