Juyin Mulki: Tinubu Ya Tsallake Rijiya, An Gano Wani Mugun Shiri da Sojoji Suka Yi na Kwace Aso Rock
- An sake bankado shirin da sojojin da aka kama d'suka yi da nufin kwace mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu da karfin bindiga
- Wani rahoton bayan fage da ya sake bulla, ya nuna yadda wadanda ake zargin suka kitsa kwace fadar shugaban kasa da cafke Tinubu ko kashe shi
- Kwamitin da ya gudanar da bincike kan lamarin, ya ce da sun yi nasara, cikin kankanin lokaci za su karbe iko a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Najeirya - Yayin da ake shirye-shiryen fara bukukuwan karamar Sallah a Najeriya, an kara samun sababbin bayanai kan yunkurin da aka yi na kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
A bara ne dai aka fara jin kishin-kishin din cewa wasu dakarun sojoji da hadin bakin manyan mutane a Najeriya sun kitsa yiwa Shugaba Tinubu juyin mulki amma asirinsu ya tonu.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta bankado wasu sababbin bayanai da ke nuna cewa wasu da ake zargi da shirin juyin mulki sun tsara kai wani gagarumin hari domin kwace iko a Najeriya.
Bincike ya nuna cewa bayan shirin kashe su da aka ruwaito a baya, akwai wani tsari mai zurfi da wadanda ake zargi suka tsara domin kwace Fadar Shugaban Kasa tare da rusa tsarin jagoranci na kasar.
Shirin karbe Aso Rock da kama Tinubu
Rahotanni sun nuna cewa babban abin da suka sa gaba shi ne mamaye Fadar Shugaban Kasa a Abuja, wacce ita ce cibiyar mulkin Najeriya mafi tsaro, domin kama Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.
Haka kuma, an ce shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas suna cikin wadanda ake shirin kamawa ko ma a kashe su.
Shirin da aka yiwa manyan jami’an tsaro
Masu bincike sun ce shirin ya hada da kai hari kan manyan jami’an tsaro kamar mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, tsohon sufeto janar na ‘yan sanda Kayode Egbetokun, da daraktan DSS, Adeola Ajayi.
An ce an ware wasu jami’ai na musamman da za su jagoranci kai hare-haren, ciki har da wata tawaga da aka kira “decapitation unit”, wacce za ta jagoranci rusa manyan shugabanni.
Rahotanni sun nuna cewa an tsara shirin ne kamar cikakken juyin mulkin soja, inda aka raba ayyuka ga tawagogi daban-daban domin kwace muhimman wurare a lokaci guda.
Yayin da wata tawaga za ta kai hari kan Aso Rock, wata kuma za ta kwace Barikin Neja, wacce ke kusa da fadar shugaban kasa kuma ke dauke da manyan hafsoshin soja.
A nan ne aka tsara kashe manyan hafsoshin soja ciki har da babban hafsan tsaro da shugabannin rundunonin soja.

Source: Twitter
Kwace filin jirgin sama da cibiyoyi
Sauran tawagogin kuma an ba su umarnin kwace cibiyar rundunar sojojin Najeriya da ke Garki a Abuja, da kuma filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, domin katse hanyoyin shiga da fita daga babban birnin.

Kara karanta wannan
Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri
Masu bincike sun ce idan da wannan shiri ya yi nasara, da cikin ‘yan sa’o’i kadan masu shirin juyin mulkin za su mallaki ikon tafiyar da Abuja gaba daya, cewar rahoton Premium Times.
Yadda aka shirya kashe Janar Musa
A baya, kun ji cewa ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa yana cikin mutanen da masu yunkurin juyin mulki suka sanya a jerin waɗanda za a harbe.
Wannan bayani na zuwa ne kwanaki bayan an tabbatar da cewa wasu daga cikin jami’an soji 16 da aka kama a 2025 za su fuskanci shari’a bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
A wata hira da aka yi da shi kan lamarin, Janar Musa ya bayyana mutanen da ake zargi da shirya juyin mulkin a matsayin marasa hankali.
Asali: Legit.ng

