Sojoji Sun Kashe Boko Haram Kusan 100 Suna Shirin kai Hari ana Gobe Sallah
- Rundunar sojin Najeriya ta samu gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan Boko Haram yayin da suka yi musayar wuta a jihar Borno
- Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun shirya kai wani mummunan hari ne a daidai lokacin da aka fara shirye-shiryen bikin sallah
- Sojojin Najeriya sun fitar da sunayen wasu daga cikin manyan 'yan ta'addan da aka tabbatar da kashe su har lahira yayin farmakin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Dakarun rundunar hadin gwiwa ta yankin Arewa maso Gabas, wato Operation Hadin Kai (OPHK), sun samu nasarar dakile wani hari da ‘yan ta’adda suka kai da asubahin ranar Laraba a sansanoninsu da ke Malam Fatori.
‘Yan ta’addan, wadanda suka taso da yawa a kafa tare da amfani da jirage marasa matuka masu dauke da makamai domin kai hari sun gamu da turjiya mai karfi daga dakarun.

Source: Twitter
Jami'in yada labaran Operaton Hadin Kai, Laftanar Kanal Sani Uba ya fadi nasarorin da suka samu yayin harin a wani sako da ya fitar a Facebook.
Yadda sojoji suka kashe Boko Haram
Saboda cikakken shiri da fahimtar salon yaki, dakarun Najeriya sun riga sun hango yiwuwar harin, inda suka shirya dabarun yaki tare da kai farmaki domin murkushe ‘yan ta’addan gaba daya.
Ta hanyar amfani da ingantacciyar hanyar sarrafa makami, hadin kai da kuma kwarewar dabarun yaki, an fatattaki maharan tare da kashe akalla ‘yan ta’adda 80 a yayin fafatawar.
Harin ya kara samun karfi daga taimakon jiragen sama na rundunar, tare da kai hare-haren sama daga abokan hadin gwiwa na Nijar, wanda ya kara matsa lamba kan ‘yan ta’addan da ke gudu.
Makaman da sojoji suka kwato
Sojoji sun sanar da cewa sun kwato makamai da kayan yaki masu yawa, ciki har da bindigogi kirar AK-47 guda 52, bindigogin PKT guda 8, makaman RPG guda 7, manyan bindigogi masu nauyi guda 5 (GPMG).

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa sun kwato harsasai sama da 3,000, bom din RPG guda 21, bama-bamai na gida guda 9, na’urorin sadarwa da kuma sassan jirage marasa matuka da ‘yan ta’addan suka yi amfani da su.
Sunayen Boko Haram da aka kashe
Farmakin ya yi sanadin kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan ta’adda guda uku, wato Malam Abdulrahman Gobara, Malam Ba Yuram da Abou Ayyuba, wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da jagorantar harin.
Haka kuma, wasu fitattun ‘yan ta’adda da aka kashe sun hada da Zarkawi, Ba Bunu, Rawa Fannami, Abowor Suwurti, Bulama Mil, Abu Aisha, Suleimana, Abu Rijal, Abu Ali, Abba Gana Kawiyya da Ahmodu Hirasama.
An ce kashe wadannan shugabanni da mayaka ya kawo babbar barazana ga tsarin jagoranci da karfin aiki na ‘yan ta’addan a jihar Borno.
Tinubu ya magantu kan harin Borno
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tir da harin da ake zargi 'yan Boko Haram ne suka kai birnin Maiduguri.
Shugaban kasar ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun kai harin ne sakamakon matsin lambar da dakarun Najeriya ke musu a yankunan Borno.
Bola Tinubu ya umarci hafsoshin tsaro da su koma Maiduguri domin gano wadanda suka shirya harin kunar bakin waken da murkushe su.
Asali: Legit.ng


