Bayan Sanarwar Saudiyya, Sarkin Musulmi Ya Fadi Ranar da Za a Yi Karamar Sallah a Najeriya
- Fadar Sarkin Musulmi ta bayyana cewa ba ta samu rahoton ganin jinjirin watan karamar Sallah ba a fadin Najeriya
- Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III, ya bayyana cewa za a cika azumi 30, sannan a yi sallar idi ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026
- Ya kuma taya al'ummar musulmi murnar zagayowar karamar Sallah, inda ya bukaci su yi amfani da wannan dama wajen yi wa Najeriya addu'a
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Sokoto, Nigeria - Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar II, ya sanar da ranar da za a yi idin karamar Sallah a Najeriya.
Sarkin, wanda shi ne shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya ya ce ba a samu rahoton ganin jinjirin watan Shawwal, 1447AH ba a yau Laraba, 29 ga Ramadan.

Kara karanta wannan
29 ko 30: Malamin addini ya riga sarkin Musulmi, ya sanar da ranar karamar Sallah a Najeriya

Source: Facebook
Hakan na kunshe a wata sanarwa da shafin Daular Usmaniyya ya wallafa a Facebook mai dauke da sa hannun Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin harkokin addini na fadar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaidu.
Ba a ga watan Sallah ba a Najeriya
Sanarwar ta bayyana cewa kwamitin ganin wata na fadar Sarkin Musulmi bai samu sahihin rahoton ganin wata daga ko'ina ba a fadin Najeriya.
Bisa ga wannan bayani, ranar Alhamis, 19 ga watan Maris, za ta zama ranar da za a cika azumi na 30 a watan Ramadan.
Sarkin Musulmin ya ayyana ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026 a matsayin ranar karamar Sallah, watau 1 ga watan Shawwal 1447AH.
Ya bukaci Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na bikin Karamar Sallah wajen yin addu'o'in neman zaman lafiya, hadin kai, da dorewar ci gaba a Najeriya.
Sanarwar da Aarkin Musulmi ya fitar
Sanarwar ta ce:
"Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar CFR, mni, kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya karbi rahoton duban wata, wanda ya nuna ba a ga jinjirin wata ba a yau Laraba.
"Bisa haka, ya ayyana ranar Juma’a, 20 ga Maris, 2026, a matsayin 1 Shawwal 1447AH (Ranar Karamar Sallah). Ya kuma taya al'ummar Musulmin Najeriya murnar zagayowar wannan lokaci, sannan yana yi musu fatan samun shiriya da albarka.
"Ya kuma bukaci a ci gaba da addu'o'in neman zaman lafiya, ci gaba, da bunkasar kasar nan. Haka zalika, yana yi wa musulmi fatan alheri da shagalin Karamar Sallah lafiya. Allah (SWT) Ya karbi ayyukanmu na ibada, amin."

Source: Facebook
Ba a ga wata ba a Saudiyya
A dazu, kun ji cewa Saudiyya ta tabbatar da cewa ba a samu sahiihin rahoton ganin jinjirin watan Shawwal na shekarar 1447AH ba a yau Laraba, 29 ga watan Ramadan.
Bisa haka, masarautar Saudiyya ta bayyana cewa musulmi za su cika azumi 30 cif a wannan shekara, tare da ayyana ranar Juma'a, 20 ga watan Maris, 2026 a matsayin ranar karamar Sallah.
Hakan na kunshe ne a sanarwar da hukumar kula da masallacin Harami da Masallacin Annabi SAW, ta fitar bayan kammala tattara bayanai.
Asali: Legit.ng
