'Ku Yi Koyi da Annabi SAW': Malami ga Sanusi II, Aminu Bayero kan Hawan Sallah a Kano
- Wani malamin addini a Kano ya roƙi Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II su guji rikici kan shirin gudanar da hawan Sallah
- Ya yi gargadin cewa dagewa kan gudanar da hawa biyu a lokaci guda na iya haddasa rikici, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya ga cigaba
- Malamin ya buƙaci gwamnati da jami’an tsaro su dauki matakan kariya, yana mai cewa duk shugaba za a yi masa hisabi a ranar lahira kan ayyukansa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani malamin addinin Musulunci a Kano, Sheikh Yahya Maimota, ya roƙi Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah.
Malamin ya bukaci sarakunan da su nuna hakuri kan batun hawan Sallah da ake shirin yi a jihar Kano.

Source: Facebook
Malamin ya bayar da wannan shawara ne yayin tafsirin Ramadan da ya gabatar a masallacin Juma’a na Sabo Dankoli da ke Sharada, cikin birnin Kano wanda ya yada a shafinsa na Facebook.
Hawan salla: Malami ya shawarci Sanusi II, Bayero
Gargadin ya biyo bayan ƙarin tashin hankali da damuwa kan yiwuwar rikici, sakamakon dagewar sarakunan biyu na gudanar da hawan Sallah a lokaci guda.
Sheikh Maimota ya tunatar da shugabanni da al’umma muhimmancin zaman lafiya kamar yadda Annabi Muhammad SAW ya koyar a cikin hadisai da koyarwarsa.
Ya ce:
“Kada ku yi fatan yaki ko haduwa da makiya; ku nemi zaman lafiya da natsuwa a cikin al’umma."
Malamin ya kara da cewa duk wani rikici na iya lalata zaman lafiyar da Kano ke morewa a halin yanzu, wanda ya kasance mai rauni.
Ya bayyana cewa tashi lafiya, rayuwa cikin kwanciyar hankali, da samun abinci suna daga cikin manyan ni’imomin da Allah SWT ke bai wa bayinsa.
Shawarar malamin ga shugabanni a Kano
Malamin ya kuma bukaci shugabanni su fifita kare rayuka da dukiyoyi, yana mai cewa cigaba yana samuwa ne kawai a inda zaman lafiya ke wanzuwa.
A cewarsa, martabar Kano a matsayin cibiyar kasuwanci ba za ta dore ba tare da zaman lafiya ba, domin ilimi da kasuwanci suna bukatar tsaro.
Ko da yake ya amince da muhimmancin al’adun hawan Sallah, ya ce idan hakan zai kawo barazana ga tsaro, ya kamata a dakatar da shi.
Ya kara da cewa har yanzu shari’ar sarautar na gaban kotu, kuma ba a yanke hukunci ba kan rikicin da ake fama da shi.

Source: Original
'Yadda sarakunan baya suka fifita zaman lafiya'
Malamin ya tunatar da cewa a baya sarakuna kan dakatar da hawan Sallah idan akwai yiwuwar rikici, yana mai cewa abin damuwa ne yanzu akasin haka.
Ya bukaci gwamnatin Kano da jami’an tsaro su dauki matakan kariya domin hana tabarbarewar tsaro da ka iya tasowa.
Ya yi gargadin cewa ko da an tura jami’an tsaro da yawa, rikicin cikin masarauta na iya haddasa tashin hankali mai tsanani.
Kano: An fadi wanda zai jagoranci sallar Idi
An ji cewa Gwamnatin Kano ta yi magana kan hawan Daushe da sauran hawan dawakai saboda rahotannin sirri da aka samu a jihar.
Gwamnatin ta ce ta dakatar da wasu bukukuwan da ake yi bayan gano wasu na shirin tayar da tarzoma a yayin bikin sallah a Kano.
Ta ce Sarki Muhammad Sanusi II ne zai jagoranci Hawan Idi, yayin da aka soke Hawan Fanisau da Dorayi domin tabbatar da tsaron jama'a da dukiyoyinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


