Bayan Shekaru 4 a Garkame, Gwamna Ya Umarci Bude Babban Masallacin Juma’a

Bayan Shekaru 4 a Garkame, Gwamna Ya Umarci Bude Babban Masallacin Juma’a

  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ba da umarnin sake bude babban masallacin Juma'a bayan shekaru hudu a kulle
  • An rufe masallacin tun 2022 saboda rikicin shugabanci da ya dabaibaye limancin masallacin da ake faragabar barkewar rikici
  • An umurci Sheikh Abubakar Muhammed Abbas da ya ci gaba da jagorantar sallar Juma’a kamar yadda yake yi a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikare, Ondo - Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ba da umarnin sake bude babban masallacin Juma'a bayan shekaru hudu.

Gwamna ya ba da umarnin ne kan masallacin Ikare-Akoko wanda aka rufe tun ranar 18 ga Oktoba, 2022 a yankin.

Gwamna ya sake bude masallaci bayan shekaru 4
Gwamna Lucky Aiyedatiwa tare da Sarakunan Ikare da limamai yayin sake bude masallacin Juma'a a Ondo. Hoto: Ikare Kingdom, Ondo State Nigeria.
Source: Facebook

Gwamna ya sake bude babban masallacin Juma'a

Gwamnan ya bayyana hakan ne a garin Akure yayin wani taron buda baki na Ramadan da ya yi da al'umma, kamar yadda Masarautar Ikare ta wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Sanusi II ko Aminu Ado?: An fadi 'sarkin' da zai jagoranci hawan Sallah a Kano

Shafin masarautar ya yabawa Gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa kan sabon babi a tarihin Ondo bayan sake bude Babban Masallacin Ikare.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin watan Ramadan a matsayin lokaci na tunani, sabunta imani da kuma kyautata halaye.

Taron ya gudana ne tare da hadin gwiwar gwamnatin Ondo da Hukumar Jin Dadin Musulmi ta jihar.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya umurci Sheikh Abubakar Muhammed Abbas, wanda shi ne babban limamin garin kafin rufe masallacin, da ya koma ya ci gaba da jagorantar ibada.

Ya ce an dauki wannan mataki ne domin karfafa hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar yankin.

A yayin sanarwar, gwamnan ya ce da kasancewar Sarki da manyan malamai a wurin, ya ayyana cewa an bude masallacin a hukumance.

Ya kara da cewa babban limamin zai jagoranci salla a cikin yanayin mutunta juna da hadin kai tsakanin al’ummar Musulmi.

Gwamna ya shawarci Musulmi bayan bude masallacin da aka rufe na shekaru 4
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo. Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa.
Source: Twitter

Yaushe aka rufe masallacin Juma'a a Ikare?

Rahotanni sun nuna cewa an nada Sheikh Abubakar Muhammed Abbas a matsayin Mataimakin shugaban kungiyar limamai da malaman An sake Ondo.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutu don bukukuwan karamar Sallah

Kwamitin da ya nada shi ya samu jagoranci daga Sheikh Shehu Batuta wanda shi ne babban malami a Ondo.

An rufe masallacin ne a lokacin marigayi tsohon gwamna Oluwarotimi Akeredolu domin dakile rikicin shugabanci da ya kunno kai a garin a 2022.

Ya ce:

“Wannan Ramadan yana tunatar da mu cewa zaman lafiya, tausayi, kauna da jin kai su ne ginshikan al’umma mai cike da jituwa.”

Ya kara da cewa yana yaba wa al’ummar yankin bisa goyon baya da hadin kai da suka nuna inda ya shawarce da su kara hakuri.

An sake bude masallaci mai shekaru 217

A wani labarin mai kama da wannan, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara da Gwamna Babagana Zulum na Borno sun halarci taron bude masallacin Juma'a.

An bude masallacin Imam Gambari da aka gyara a birnin Ilorin wanda ya shafe shekaru fiye da 200 a jihar a kulle.

Masallacin da aka kafa tun 1808, yana daya daga tsofaffin cibiyoyin ilimin addini, yanzu an mayar da shi na zamani domin ci gaba da ibada a ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.