Ana Neman Karawa Ma'aikatan Najeriya Karin Albashin Sama da N150,000
- Rahoto ya nuna cewa kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta fara sabuwar fafutukar nemawa ma'aikatan Najeriya karin albashi daga gwamnati
- 'Yan kwadago sun bayyana cewa ma'aikata na shan wahala sosai duk da karin mafi karancin albashi da aka yi zuwa N70,000 a baya
- Kungiyoyin kwadago da suka nemi karin albashin sun nemi zama da ofishin shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya domin samun mafita
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Majalisar JNPSNC karkashin kungiyoyin kwadago ta kasa ta bukaci a kara mafi karancin albashi zuwa N154,000, karin kashi 120 na albashi da alawus-alawus ga ma’aikatan gwamnati a Najeriya.
Rahoto ya nuna cewa kungiyar ta ce wannan sabuwar bukata na da nufin rage abin da ta kira “rayuwar bauta” da ma’aikata ke ciki a halin yanzu a kasar nan.

Source: Twitter
Wasikar da 'yan kwadago suka fitar
Punch ta wallafa cewa 'yan kwadago sun mika bukatar ne a cikin wata wasika da aka aike wa ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, mai dauke da kwanan wata 12 ga Maris 2026, mai lamba JNPSNC/Gen/Cor/Vol 1/163.
Taken wasikar shi ne bukatar gaggawa ta kara albashi da alawus-alawus ga ma’aikatan gwamnati a Najeriya da kuma amincewa da biyan kudin ritaya ga ma’aikatan da ke barin aiki.
Shugaban JNPSNC, Benjamin Anthony, da sakatarensa na kasa, Olowoyo Gbenga ne suka sanya hannu a wasikar da suka turawa gwamnati.
An nemi karin albashi a Najeriya
'Yan kwadago sun ce sun rubuta wasikar cikin girmamawa domin jawo hankalin ofishin shugaban ma'aikata kan bukatar gaggawa ta kara albashi da alawus-alawus ga dukkan ma’aikatan gwamnati.
Wasikar ta ce:
“Duk da gudunmawar da suke bayarwa, ma’aikatan gwamnati na fuskantar tsananin wahalar tattalin arziki sakamakon tashin farashin kayayyaki.”
Matsalar da ma'aikata ke fuskanta
Majalisar ta ce a tsawon lokaci, Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki mai tsanani wanda ya hada da hauhawar farashi, karin kudin man fetur, tashin kudin sufuri, karin farashin abinci, kudin haya, magani da kudin makaranta.
Ta kara da cewa wadannan abubuwa sun rage darajar albashin ma’aikata, lamarin da ke sa ya zama da wuya ga yawancin ma’aikata su rayu cikin walwala.

Source: Twitter
A kan maganar karin albashi da aka yi a baya, 'yan kwadago sun nuna cewa karin albashin da aka yi bai yi daidai da yanayin tattalin arzikin kasar nan ba.
N154,000: Sabon albashin da ake so
'Yan kwadago sun bukaci a fara tattaunawa nan take tare da hukumar tsara albashi da kudin shiga da sauran kwamitoci domin cimma yarjejeniya kan karin albashi da alawus-alawus.
AIT ta rahoto sun ce:
“A samar da sabon tsarin albashi wanda zai tabbatar da cewa mafi karancin albashin ma’aikaci zai kasance N154,000 a wata ga ma’aikatan gwamnatin tarayya."
NLC ta gargadi Tinubu kan haraji
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kwadago ta NLC ta yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu gargadi game da dokokin haraji da ya kawo.

Kara karanta wannan
Luguden wutar Amurka da Isra'ila ya yi barna a kasar Musulunci ta Iran, sama da mutum 100 sun mutu
NLC ta bukaci shugaban kasar ya dakatar da fara aiki da dokokin da ya kaddamar a farkon shekarar 2026 bayan amincewa da su a 2025.
'Yan kwadago sun ce ma'aikatan gwamnati da masu zaman kansu ne manyan masu biyan haraji a kasar nan amma haka aka yi dokokin ba tare da tuntubarsu ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

