Yaki Ya Yi Zafi, Isra'ila Ta Kashe Babban Kwamanda a Iran

Yaki Ya Yi Zafi, Isra'ila Ta Kashe Babban Kwamanda a Iran

  • Isra'ila na ci gaba da farmakar manyan kwamandojin rundunonin tsaro a kasar Kamhiriyar Musulunci ta Iran yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a Gabas ta Tsakiya
  • Rundunar sojojin Isra'ila ta yi ikirarin kashe babban kwamandan dakarun Basij yayin wasu hare-hare da ta kai a daren ranar Litinin, 16 ga watan Maris 2026
  • Sai dai, har zuwa ba a ji daga bangaren mahukunta daga Iran ba game da gaskiya ko rashin gaskiyar ikirarin da Isra'ila ta yi na kashe Gholamreza Soleimani

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa ta kashe kwamandan dakarun Basij da ke aiki a karkashin rundunar IRGC, Gholamreza Soleimani.

Isra'ila ta yi ikirarin kashe Gholamreza Soleimani ne a wani hari da ta kai a daren Litinin, 16 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi

Isra'ila ta ce ta kashe Gholamreza Soleimani
Shugaban dakarun Basij na Iran, Gholamreza Soleimani Hoto: Atta kenare
Source: Getty Images

Isra'ila ta yi ikirarin kashe babban kwamandan Iran

Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana kisan na Gholareza Soleimani a ranar Talata, 17 ga watan Maris 2026 a shafinta na X.

Isra'ila ta bayyana cewa iƙirarin kisan Soleimani wani “babban rashi ne” ga “tsarin ba da umarni da iko” na Iran, kuma ta yi alkawarin “ci gaba da amfani da ƙarfi” kan kwamandojin Iran.

Sai dai, har ya zuwa yanzu, babu wani sharhi daga ɓangaren Iran kan kisan kwamandan na dakarun Basij.

Wane ne Gholamreza Soleimani?

Tashar Aljazeera ta tattaro wasu abubuwan da ya kamata a sani game da kwamandan na Iran:

An haife shi a shekarar 1964, Gholamreza Soleimani ya shiga rundunar IRGC ta Iran tun yana saurayi kuma ya ci gaba da samun matsayi a cikinta.

Ya yi aiki a matsayin kwamandan bataliya lokacin yaƙin Iran da Iraƙi, sannan daga baya ya jagoranci rukunonin IRGC da dama.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fara neman sauran ƴan ƙunar baƙin wake a Borno, an nemi daukin jama'a

Tun daga shekarar 2019, ya kasance shugaban dakarun Basij, wata runduna a ƙarƙashin IRGC mai kimanin mambobi 450,000, wanda hakan ya sa ya zama babban jigo a tsarin tsaron cikin gida na Iran.

Kasancewarsa mai kishin kare gwamnatin Iran, Soleimani yana fuskantar takunkumi daga ƙasashe da ƙungiyoyin Yamma da dama, ciki har da Amurka, Tarayyar Turai (EU), Burtaniya, da Canada.

Israila ta yi kashe babban kwamandan dakarun Basij na Iran
Dakarun rundunar Basij ta kasar Iran Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Ministan tsaron Isra'ila ya yi magana

Ministan tsaron Isra'ila, Katz, ya fitar da wata sanarwa da ke nuna kashe Gholamreza Soleimani.

“Ana kashe shugabannin gwamnatin Iran sannan ana rugurguza ƙarfinsu."
“Rundunarmu tana aiki da ƙarfin gaske don ci gaba da kai hari da kuma kawo ƙarshen ƙarfin makamai masu linzami gami da muhimman wuraren dabarun yaƙi.”

- Israel Katz

Hare-haren Isra'ila sun kashe mutane a Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa hare-haren da Amurka da Isra'i'a ke kai wa lardin Kurdistan na Iran, ya yi sanadiyar kashe akalla mutane 112 tare da raunata wasu mutane 969.

Shugaban sashen agajin gaggawa na lardin ya bayyana cewa mutane da dama sun jikkata sakamakon hare-haren jiragen sama da makamai masu linzami.

Hare-haren na daga cikin manyan farmakin da ake kai wa yankin wanda yake a Arewa maso Yammacin Iran tun bayan fara yakin a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng