Sojoji Sun Fara Neman Sauran Ƴan Ƙunar Baƙin Wake a Borno, An Nemi Daukin Jama'a

Sojoji Sun Fara Neman Sauran Ƴan Ƙunar Baƙin Wake a Borno, An Nemi Daukin Jama'a

  • Sojojin Najeriya sun tabbatar da hare-haren bama-bamai da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai Maiduguri a ranar Litinin, 16 ga watan Maris, 2026
  • Lamarin ya girgiza mazauna birnin da Arewacin Najeriya baki daya, musamman ganin yadda yawanci wadanda aka kashe suna kokarin buda-baki
  • Rundunar sojojiin Najeriya ta bayyana cewa sun samu bayanai game da karin 'yan kunar bakin wake da aka turo jihar domin tayar da hankula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Hedikwatar rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas, wato 'operatin hadin kai', ta tabbatar da cewa an samu jerin fashewar bama-bamai a Maiduguri.

Lamarin ya faru da karfe 7.05 na yamma a cikin birnin Maiduguri a daren Litinin, 16 ga Maris, 2026, a lokacin da al’umma ke gudanar da buda baki.

Kara karanta wannan

Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri

Rundunar sojin Najeriya ta mika ta'aziyya ga al'ummar Borno
Shugaban sojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Waidi Sha'abu Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

A sakon da rundunar ta wallafa a shafin X, ta ce wuraren da aka kai wa hari sun hada da yankin Post Office, kasuwar Monday da kuma kofar shiga asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH).

Sojoji sun yi magana game da harin Borno

Rundunar ta ce ‘yan ta’addan sun zabi wadannan wurare ne domin samun yawan jama’a da nufin haddasa asarar rayuka da tayar da hankalin al’umma.

A wata sanarwa da Laftanar Kanar Sani Uba, jami’in yada labarai na rundunar Operation hadin kai ya sanya wa hannu, rundunar ta 'yan ta'addan sun kudiri niyyar tayar da hankulan 'yan Maiduguri.

Sanarwar ta kara da cewa amma jami’an tsaro sun dauki matakin gaggawa domin shawo kan lamarin da kuma dakule wadansu hare-hare a nan gaba.

Sojoji sun fara farautar sauran ‘yan ta’adda

Bayan aukuwar lamarin, sojojin tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sanda musamman bangaren kula da abubuwan fashewa (EOD), sun isa wuraren da abin ya shafa cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Harin Maiduguri ya zubar da jinin sama da mutum 100, 23 sun mutu nan take

Sojoji sun nemi dauki don gano sauran yan ta'adda a Borno
Taswirar jihar Borno inda aka kai mugayen hare-hare Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sun killace yankunan tare da hana zirga-zirga domin kaucewa karin hadari ga jama’a yayin da ake ci gaba da bincike domin tabbatar da tsaron wuraren.

Haka kuma, jami’an agajin gaggawa ciki har da na NEMA da sauran ma’aikatan lafiya sun yi kokarin kwashe wadanda suka jikkata zuwa manyan asibitocin jihar.

Binciken farko ya nuna yiwuwar cewa ‘yan ta’addan sun tura mutane da dama cikin birnin domin kai irin wadannan hare-hare a lokaci guda.

Saboda haka, hukumomin tsaro sun kara tsaurara sintiri da sanya ido a fadin Maiduguri, tare da daukar matakan gano sauran wadanda ake zargi da hana aukuwar karin hare-hare.

Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu amma su kasance cikin shiri, su guji wuraren da ke da cunkoso idan ba dole ba.

Haka kuma rundunar ta bayyana cewa akwai bukatar mazauna jihar su rika kai rahoton duk wani motsi na shakku ga hukumomin tsaro mafi kusa.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan fashewar bama bamai a Maiduguri ana cikin shan ruwa

Rundunar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tana mai jaddada kudirinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sakon Zulum bayan harin Maiduguri

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana matukar takaici da tagwayen hare-hare da ƴan Boko Haram suka kai Maiduguri.

Fashewar bama-baman ya auku a kasuwar Monday da kofar asibitin koyarwa ta Maiduguri a ranar Litinin, 16 ga Maris, 2026 lamarin da ya ruda jama'a da ke kokarin buda-baki.

An kashe mutane tare da jikkata da dama daga cikin bayin Allah da suke kan hanyar da kasuwar, yayin da jami’an tsaro suka shiga aikin ceto mutanen da suka jikkata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng