Kwankwaso Ya Tura Sako ga Shugaban Ƙasa game da Harin Bama Bamai a Maiduguri

Kwankwaso Ya Tura Sako ga Shugaban Ƙasa game da Harin Bama Bamai a Maiduguri

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya nuna alhini kan hare-haren kunar bakin wake a Maiduguri
  • Rahotanni sun ce mutane 23 sun mutu, sama da 100 sun jikkata a harin bama-bamai da aka kai Maidugurin jihar Borno
  • Ya bukaci gwamnati da sojoji su dauki matakin gaggawa domin dakile ta’addancin da ya ki ci, ya ƙi cinye wa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan hare-haren kunar bakin wake da suka girgiza birnin Maiduguri.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Kwankwaso ya ce hare-haren Maiduguri da suka yi sanadin mutuwar akalla mutane 23, tare da jikkata fiye da mutum 100 abin takaici ne.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fara neman sauran ƴan ƙunar baƙin wake a Borno, an nemi daukin jama'a

Kwankwaso ya tura sako ga shugabanni kan harin Maiduguri
Gwamna Babagana Zulum, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, Shugaban ƙasa Bola Tinubu Hot: The Governor of Borno state/Rabiu Musa Kwankwaso/Jagaban Army
Source: Facebook

A sabon da ya wallafa a shafin sa na Facebook, Sanata Kwankwaso ya bayyana matukar alhini kan kashe-kashen da ke ci gaba da girgiza jama'ar kasar nan.

Kwankwaso ya yi takaicin harin Maiduguri

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta tabbatar da harin da ya kashe bayin Allah da dama yayin da wasu ke kwance rai a hannun Allah.

A sakon da Kwankwaso ya fitar game da lamarin, ya ce:

“Na yi matukar bakin ciki da wadannan munanan hare-hare na kunar bakin wake da suka afku a Maiduguri, wanda ya yi sanadin rasa rayukan mutane 23 marasa laifi tare da jikkata sama da 100.”

Kwankwaso ya kara da cewa, wadannan hare-hare na baya-bayan nan, tare da wasu da suka gabata a jihar Borno, na nuna sake dawowar barazanar ta’addanci.

Kwankwaso ya aika sako ga Shugaba kasa

Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce waɗannan hare-hare za su iya tarwatsa zaman lafiya da aka shafe shekaru ana ƙoƙarin farfaɗo da shi.

Kara karanta wannan

Abin da ake cewa kan Trump ya gargadi Tinubu bayan harin Maiduguri

"Wadannan hare-hare sun nuna wata barazana mai tayar da hankali na sake dawowar ta’addanci marar ma’ana, wanda ke barazana ga zaman lafiyar al’ummominmu. Ba za mu taba lamunta ba.”

Kwankwaso ya jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta dauki mataki mai karfi maimakon nuna sakaci ko jinkiri wajen magance matsalar tsaro.

Kwankwaso ya ce ya kamata a kawo karshen hare-haren ƴan ta'adda
Tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa, Rabi'u Musa Kwankwaso yana jawabi Hoto: Rabi'u Musa Kwankwaso
Source: Facebook

Ya ce:

“Yanzu ba lokacin sakaci ko kauce wa gaskiya ba ne. Dole ne a bai wa dakarunmu cikakken iko da kayan aiki domin su dauki matakan da suka dace kan wadannan makiyan Najeriya.”

Ya bukaci gwamnatocin tarayya da na jihohi da su hada kai wajen samar da dukkanin kayan aiki da goyon bayan da ake bukata domin bai wa jami’an tsaro damar murkushe kungiyoyin ta’addanci gaba daya.

Kwankwaso ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, da wadanda suka jikkata, tare da daukacin al’ummar jihar Borno.

Zulum ya yi magana game da harin Maiduguri

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana matukar takaici da tagwayen hare-hare da ƴan Boko Haram suka kai Maiduguri.

Kara karanta wannan

Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri

Fashewar bama-baman ta auku a kasuwar Monday da kofar asibitin koyarwa ta Maiduguri a ranar Litinin, 16 ga Maris, 2026 inda aka kashe bayin Allah da dama.

Harin ya daga hankalin jama'a sosai, sai dai rundunar ƴan sandan jihar ta ce an shawo kan al'amarin kuma ana ɗaukar matakan kare aukuwar irin wannan hari a nan gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng