Da Gaske Gwamna Abba Ya Ce Sanusi II ba zai Yi Hawan Sallah a Kano ba?
- Gwamnatin Kano ta fito ta yi karin bayani game da wani sako da ya karade kafafen sada zumunta game da hawan sallah a jihar a 2026
- Sanarwar da aka rika yadawa ta nuna cewa gwamnatin ta ce ba mai martaba Muhammadu Sanusi II ne zai yi hawan sallah a jihar ba a bana
- Hakan na zuwa ne bayan mai martaba Aminu Ado Bayero ya fitar da sanarwa ga rundunar 'yan sanda game da shirin hawan sallah da zai yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Kamar yadda aka yi a 2025, a shekarar 2026 ma an fara ce-ce-ku-ce game da shirin hawan sallah a jihar Kano yayin da azumi ke shirin karewa.
Gwamnatin jihar Kano ta yi karin haske game da wata sanarwar da ke nuna cewa wai ta ce ba mai martaba Muhammadu Sanusi II ne zai jagoranci hawan sallah a 2026 ba.

Source: Facebook
Kwamishinan yada labarai a gwamnatin Abba Kabir Yusuf, Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya yi karin haske a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
Sanusi II zai yi hawan sallah a Kano?
Kwamishinan yada labaran Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya ya karyata wata takarda da ke yawo cewa gwamnati ta ce ba mai martaba Muhammadu Sanusi II ne zai jagoranci hawan sallah ba.
An fitar da takardar ne domin nuna goyon bayan gwamnatin Kano ga shirin hawan sallah da mai martaba Aminu Ado Bayero ya ce zai yi, amma duk da haka gwamnati ta ce ba ruwanta.
Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce:
"An ja hankalina zuwa wata sanarwar manema labarai da ake cewa ni ne na fitar da ita. Ina sanar da daukacin jama’a cewa wannan sanarwa ba daga ofishina ta fito ba, kuma ba a fitar da ita a madadin gwamnatin jihar Kano ba.

Kara karanta wannan
"Da na fuskanci kaskanci," Sanusi II ya tuna lokacin da aka cire shi daga sarkin Kano
"Wannan wani aiki ne na sharri da aka shirya da gangan domin yaudarar jama’a da kuma haifar da rudani."
Yayin da ya ke sanar da matakin da gwamnati ta dauka, kwamishinan ya ce:
"Na riga na kai rahoton lamarin ga jami’an tsaro domin gano wadanda ke da hannu a wannan mummunan aiki na rashin daukar alhaki da rashin kishin kasa."
Rikicin hawan sallah a Kano
Tun bayan sauke Alhaji Aminu Ado Bayero a sarautar Kano da Abba Kabir Yusuf ya yi aka fara samun takun saka game da hawan sallah a jihar.

Source: Facebook
Aminu Ado Bayero na shirya fita hawan, Sanusi II ma haka, amma a 2025 'yan sanda sun hana dukkan bangarorin fita domin hana tashin hankali.
A wannan shekarar ma, bayan Aminu Ado ya fitar da sanarwa, Leadership Hausa ta wallafa a X cewa gwamnatin Kano ta ce mai martaba Sanusi II ne zai yi hawan sallah.
Aminu Ado zai yi hawan sallah
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sarkin Kano na 15, mai martaba Aminu Ado Bayero ya sanar da jami'an tsaro cewa zai gudanar da hawan sallah.
A wasikar da ya rubuta, Sarkin ya sanar da wuraren da zai yi bukukuwan sallah domin a samar da cikakken tsaro da hana tada zaune tsaye.
Aminu Ado Bayero ya kuma yaba wa rundunar 'yan sanda bisa yadda ya ce suna jajircewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

