Duk da ba Ya Najeriya, Zulum Ya Aiko da Sako bayan Tagwayen Bama Bamai a Maiduguri

Duk da ba Ya Najeriya, Zulum Ya Aiko da Sako bayan Tagwayen Bama Bamai a Maiduguri

  • Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana matukar takaici da tagwayen hare-hare da ƴan Boko Haram suka kai Maiduguri
  • Fashewar bama-baman ta auku a kasuwar Monday da kofar asibitin koyarwa ta Maiduguri a ranar Litinin, 16 ga Maris, 2026
  • An kashe mutane tare da jikkata da dama daga cikin bayin Allah da suke kan hanyar da kasuwar, yayin da jami’an tsaro suka shiga ukun ceto

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno – Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi kakkausar suka kan fashewar bama-bamai da ta girgiza wasu sassan birnin Maiduguri da daren Litinin, 16 ga watan Maris, 2026.

Zulum, wanda ke kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah, ya bayyana harin a matsayin tsantsan rashin tausayi.

Kara karanta wannan

Manyan Kasashen duniya 2 da ke samun riba duk da yakin Iran, Amurka da Isra'ila

Bama-bamai sun fashe a Borno
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum a gidan gwamnati Hoto: The Borno state Governor
Source: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito Zulum ya ce wannan hare-hare a lokacin Ramadan ya kara wa lamarin muni, inda ya yi takaicin kashe farar hula bai gaira ba dalili.

Zulum ya yi magana kan harin Maiduguri

The Cable ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Dauda Iliya ya fitar, gwamnan ya bukaci al’umma su kara sanya ido a wuraren ibada yayin da ake tunkarar bikin Sallah.

Gwamnan ya ce:

“Na yi matukar alhini da jin labarin fashe-fashen da suka faru a wasu sassan birnin Maiduguri a daren Litinin.
“Ina alhini tare da addua ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata sakamakon wannan harin. Wannan aiki abin Allah-wadai ne, rashin imani da rashin tausayi.”

Ya kara da cewa karuwar hare-haren da ake gani na da nasaba da matsin lambar da sojoji ke yi wa ‘yan ta’adda a dajin Sambisa da sauran maboyarsu.

Kara karanta wannan

Za a yi makoki a Israi'ila, Trump na yaki da Iran, an kai hari kan yahudawa a Amurka

Zulum ya ba mutanen Borno tabbaci

Gwamnan ya bai wa al’ummar jihar tabbacin cewa jami’an tsaro sun shawo kan lamarin, inda ya ce an dauki matakan da suka dace domin hana sake aukuwar irin wannan hari a Maiduguri da sauran sassan jihar.

Ya kuma bukaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, tare da kai rahoton duk wani motsi ko abu da suka gani mai kama da barazana ga jami’an tsaro.

Bama-baman da suka tashi sun firgita jamaa
Taswirar jihar Borno inda bama-bamai suka fashe Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahotanni sun nuna cewa wasu mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da wasu da yawa suka samu raunuka sakamakon fashewar bam a kusa da kasuwar Monday da kuma kofar asibitin loyarwa na ami’ar Maiduguri.

Majiyoyi sun ce fashewar ta faru ne kusan karfe 7:02 na yamma, inda bama-baman suka tashi kusan lokaci guda tare da gigita jama'a.

Shugaban ayyuka na hukumar kashe gobara ta tarayya a jihar Borno, Mohammed Kafaran, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa sun tura jami’ansu domin tattara bayanai a wurin.

Kara karanta wannan

Nuru Khalid da malaman da aka dakatar daga wa'azi kafin Alkali Zariya

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitoci, daga ciki har da sibitin lwararru na Maiduguri, yayin da aka hangi gawarwaki a wurin.

Bama-bamai sun fashe a Maiduguri

A baya, kun ji cewa an samu fashewar wasu bama-bamai a babban birnin Maiduguri na jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da yammacin Litinin, 16 ga watan Fabrairu, 2026.

Fashe-fashen sun auku ne yayin da al'ummar Musulmi suke gudanar da buda baki yayin da ake ci gaba da gudanar da azumin watan Ramadan a sassa daban-daban na jihar.

Kararrakin fashe-fashen da aka ji a wasu wurare biyu na babban birnin sun sanya mutane sun shiga cikin firgici tare da tsorata yayin da jama'a da dama suka rasu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng