Harin Maiduguri Ya Zubar da Jinin Sama da Mutum 100, 23 Sun Mutu Nan Take

Harin Maiduguri Ya Zubar da Jinin Sama da Mutum 100, 23 Sun Mutu Nan Take

  • Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta tabbatar da cewa 'yan ta'adda sun dasa bama-bamai a wurare uku a birnin Maiduguri cikin dare
  • Yayin da ake cigaba da tattara bayanai game da barnar da harin ya yi, 'yan sanda sun ce sama da mutum 100 ne suka jikkata a halin yanzu
  • A bangaren rasa rayuka kuma, kakakin 'yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa sama da mutum 20 sun mutu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - An fara tattara bayanai game da fashewar bama-bamai da ake zargin ‘yan kunar bakin wake na kungiyar Boko Haram ne suka haddasa a Borno.

Rundunar 'yan sandan jihar ta fitar da sanarwa cewa an kai hare-haren ne a wurare uku a Maiduguri kuma ya shafi mutane kusan 150.

Kara karanta wannan

Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri

Kasuwar da aka kai harin bam Maiduguri
Jami'in tsaro a wajen da aka kai harin bam a Maiguguri. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Kakakin 'yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso ya fitar da sanarwa a X, inda ya bayyana cewa hukumomi na cigaba da bincike kan lamarin.

Wuraren da aka kai hari Maiduguri

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa hare-haren sun faru da misalin karfe 7:24 na daren 16 ga Maris, 2026, a wurare uku daban-daban a Maiduguri.

Wuraren sun hada da da Monday Market, kofar asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri da kuma daidai gadar sama da ke kusa ofishin akwatin gidan waya.

Mutanen da suka rasu a Maiduguri

Rahoton 'yan sanda ya nuna cewa mutane 23 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 108 suka samu raunuka daban-daban saboda hare-haren.

Bayan aukuwar lamarin, an tura jami’an tsaro da suka hada da rundunar ‘yan sanda, sojoji da sauran jami’an tsaro na hadin gwiwa zuwa wuraren da abin ya shafa cikin gaggawa.

'Yan sanda sun ce an killace wuraren tare da gudanar da bincike mai zurfi ta bangaren kwararrun masu dakile tashin bama-bamai na rundunar ‘yan sanda (EOD) domin tabbatar da cewa babu sauran wata barazana.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Ana cikin musayar wuta, an kama masu yiwa Iran zagon kasa a yaki da Amurka

Kiran kwamishinan 'yan sanda

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Naziru Abdulmajid, ya ziyarci wuraren domin duba halin da ake ciki kai tsaye tare da tantance matakan da ake dauka.

Al-Jazeera ta rahoto cewa ya jajanta wa wadanda abin ya shafa da iyalansu, tare da tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi ba tare da kasala ba.

Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakkun bayanai kan yadda lamarin ya faru da kuma kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci hukunci.

Taswirar jihar Borno
Taswirar jihar Borno a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Rundunar ‘yan sandan ta bukaci al’umma da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu lura, tare da gaggauta sanar da jami’an tsaro duk wani motsi ko abu da suka ga yana da shakku.

'Yan bindiga sun je filin jirgin sama

A wani labarin, kun ji cewa hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun shiga fillin jirgin Akure.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da yakin Iran da Isra'i'a, bam ya tarwatse a kusa da makarantar yahudawa

Rahotanni sun nuna cewa an kama hudu daga cikin 'yan ta'addan yayin da suka yi shirin tserewa bayan jami'an tsaro sun ankara da su.

Hukumar FAAN ta bayyana cewa an riga an mika wadanda aka kama ga 'yan sanda domin gudanar da cikakken bincike a kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng