Ana tsakiyar Yaƙin Iran da Amurka, Shugaba Tinubu Zai Shilla zuwa Ƙasar Burtaniya
- Shugaba Bola Tinubu da uwargidansa za su tashi zuwa Burtaniya a ranar Talata don kai ziyarar tarihin da ba a taba yin irinta ba cikin shekaru 37
- Sarki Charles III zai karbi bakuncin Tinubu a fadar Windsor inda za a tattauna kan harkokin tsaro da kulla yarjejeniyar kasuwanci mai tsoka
- A wannan ziyarar, Najeriya za ta samu tallafin fam miliyan 750 domin gyara manyan tashoshin jiragen ruwa na Legas da Tin Can Island
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da mai ɗakin sa, Sanata Oluremi Tinubu, za su tashi daga Abuja a gobe Talata, domin ziyarar aiki ta musamman zuwa ƙasar Burtaniya.
Sarki Charles III na Burtaniya da Sarauniya Camilla, ne suka aika wa Shugaba Tinubu da uwargidansa goron gayyata don gudanar da wannan ziyara.

Source: Facebook
Tinubu ya amsa gayyatar masarautar Burtaniya
Mai magana da yawun shugaban kasar Najeriya, Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan a sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X.
Sanarwar ta ce irin wannan ziyarar ce ta farko da wani shugaban Najeriya zai kai cikin shekaru 37, sannan Tinubu ne shugaban Najeriya na farko da zai sauka a fadar "Windsor Castle".
Sarki Charles III zai karɓi bakuncin shugaban da mai ɗakinsa a fadar Windsor daga ranar Laraba 18 ga Maris zuwa Alhamis 19 ga Maris, 2026.
Manufar wannan ziyarar ita ce ƙarfafa dangantakar dake tsakanin ƙasashen biyu da kuma lalubo hanyoyin haɗin gwiwa kan batutuwan da suka shafi shige-da-fice, kasuwanci, zuba jari, da musayar al'adu.
Abubuwan da za su faru a ziyarar Tinubu
A yayin zaman su a fadar Windsor, Sarkin zai gayyaci shugaban ƙasar domin duba wasu kayayyakin tarihi na musamman dake da alaƙa da Najeriya.

Kara karanta wannan
Iran ta sake jikawa Amurka aiki, ta ruguza shirin Shugaba Trump ana tsaka da musayar wuta
Bayan haka, za a gudanar da tattaunawa ta sirri tsakanin Sarkin da Shugaban ƙasa, sannan za su gana da ƙungiyoyin dake fafutukar wanzar da zaman lafiya tsakanin addinai.
A maraicen ranar, za a shirya gagarumin taron cin abinci na ban girma domin karrama baƙin na Najeriya.
Bayan haka, Shugaba Tinubu zai gana da Firayim Minista Keir Starmer a ofishinsa dake "10 Downing Street".
Wannan taron zai kai ga sanya hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna daban-daban dake shafar fannonin tsaro, kasuwanci, da al'adu.
Wani muhimmin sashe na ziyarar shi ne sanya hannu kan yarjejeniyar tallafin kuɗi har fam miliyan 746 tsakanin hukumar kula da kudaden shige da fice ta Burtaniya da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA).
Wannan kuɗi za a yi amfani da su ne wajen gyara manyan tashoshin jiragen ruwa na Legas (Apapa) da kuma Tin Can Island.

Source: Twitter
Tawagar da za ta raka shugaban ƙasa
Shugaba Tinubu zai samu rakiyar manyan jami'an gwamnati, ciki har da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Sauran sun haɗa da ministoci; Wale Edun (Kuɗi), Dele Alake (Ma'adinai), Idris Mohammed (Yaɗa labarai), Hannatu Musawa (Al'adu), da Dr. Jumoke Oduwole (Kasuwanci).
Hakazalika, akwai mai ba Tinubu shawara kan tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, da karamar ministar harkokin waje, Ambasada Bianca Ojukwu.
Shugaban zai dawo gida Najeriya da zarar an kammala dukkan shirye-shiryen ziyarar, kamar yadda sanarwar Bayo Onanuga ya shaida.
Karanta sanarwar Onanuga a nan kasa:
Burtaniya ta juya wa Tinubu baya
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Birtaniya ta ki amincewa da bukatar Najeriya ta mika Sanata Ike Ekweremadu ya karasa hukuncinsa a gida.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura tawaga ta musamman domin a sasanta ta yadda Ekweremadu zai koma gidan yarin Najeriya.
Sai dai wata majiya ta ce gwamnatin Birtaniya ta nuna damuwa kan yiwuwar Najeriya ta bar tsohon sanatan ya karasa hukuncinsa.
Asali: Legit.ng

