Kana So Kudinka Su Tsira? CBN Ya Jero Matakai 3 da Mutum Zai Kare Kudaden Bankinsa

Kana So Kudinka Su Tsira? CBN Ya Jero Matakai 3 da Mutum Zai Kare Kudaden Bankinsa

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ta gargadi 'yan Najeriya kan yadda za su kare kudaden da suka ajiye a asusun bankunansu
  • CBN ya bayyana hadarin bai wa wani lambobin sirri na PIN da na manhajar banki yayin da aikata laifuffukan damfara ke karuwa a Najeriya
  • Bankin ya jero muhimmam abubuwan da ya kamata masu amfani da bankuna su kiyaye don tabbatar da tsaron kudaden ajiyarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gargadi yan kasa da su killace muhimman bayanan bakunan da suke ajiyar kudadensu.

Wannan gargadi na CBN na zuwa ne yayin da harkokin damfara ta banki ke kara yawaita a sassa daban-daban na kasar nan.

Gwamnan CBN.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso Hoto: @centbank
Source: Twitter

A wani sako da CBN ya wallafa a shafinsa na X yayin da ake bikin Global Money Week 202, babban bakin ya bai wa yan Najeriya shawarar hanyar da za su kare dukiyarsu a bakuna.

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Abuja Kaduna dauke da fasinjoji ya gamu da hatsari, an samu bayanai

CBN ya shawarci 'yan Najeriya masu amfani da bankuna su kare bayanan sirrin asusun bankinsu, tare da jan hankalinsu da kada su rika bai wa kowa lambar sirri watau PIN, kalmomin sirri ko wasu muhimman bayanan banki.

Global Money Week 2026, wani shiri ne na duniya da ke wayar da kan jama’a kan yadda za su kula da kudinsu na ajiya a banki da kuma kare kansu daga yan damfara da zamba.

Shawarwarin da CBN ya ba mutane

CBN ya jaddada cewa akwai bukatar duk mai amfani da banki a Najeriya ya kula da wadannan abubuwa domin tsare kudinsa na baki, ga su kamar haka:

1. Kada a taba ba wa kowa PIN na katin ATM

2. Kada a bayyana lambobin sirri na manhajar banki

3. Kada a tura bayanan sirrin asusun banki ga wani

Bugu da kari, babban bankin ya ce ko da mutum ya kira yana cewa shi jami’in banki ne, bai kamata a ba shi irin wadannan bayanai ba.

A sakon da CBN ya wallafa, ya ce:

“Ku kare kudinku ta hanyar kare bayananku. Yayin da muke bikin Global Money Week 2026, ku tuna: kada ku taba ba wa kowa PIN, lambobin sirri ko bayanan bankinku, ko da mutum ya ce daga bankinku yake.”

Kara karanta wannan

'Ba Amurka ba ce,' an gano kasa 1 da take da makullin bude kasuwar mai ta duniya

Kudin Najeriya.
Takardun kudin Najeriya na N100, N500, da N200 Hoto: @CentBank
Source: UGC

Yadda masu zamba ke yaudarar mutane

Gargadin na zuwa ne saboda yawaitar yan damfara da zamba cikin aminci da ke yaudarar abokan huldar bankuna ta hanyoyi daban-daban, kamar kiran waya suna cewa daga banki suke da aika sakonnin SMS na bogi.

Manufar su ita ce su yaudari mutane su fadi bayanan bankinsu, wanda daga baya ake amfani da shi wajen satar kudin asusun.

Tinubu ya nada mataimakin gwamnan CBN

A wani rahoton, kun ji cewa Bola Tinubu ya nada tsohon shugaban hukumar SEC, Lamido Yuguda a matsayin Mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Wannan naɗi zai tabbata ne bayan amincewar majalisar dattawa kamar yadda sashi na 8(1) na dokar babban bankin ƙasa ta shekarar 2007 ta tanada.

Sanarwar fadar shugaban kasa ta ce Shugaba Tinubu ya zaɓi Yuguda ne sakamakon gogewarsa ta shekaru da dama a harkar banki da kasuwancin duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262