'Yan Bindiga Sun Rubuta Wasika, Sun Fadi Garuruwa 2 da Za Su Farmaka a Abuja
- Mazauna Kungaboku da Paze a Abuja sun fara barin gidajensu bayan an gano wasiƙar barazana daga 'yan bindiga a jakar makarantar wani ɗalibi
- 'Yan bindiga sun lashi takobin kai harin fansa bayan dakarun soji sun kashe kwamandansu tare da ceto mutane 19 kwanan nan a Bwari
- Rundunar 'yan sanda ta tura ƙarin jami'ai tare da shawarar mutane su sanya ido kan 'yan acaba da masu sana'ar gwangwan don tsaron lafiyarsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - A halin da ake ciki, fargaba ta mamaye garuruwan Kungaboku da Paze dake ƙaramar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
Wannan halin fargaba da suka shiga har ya sanya mazauna yankunan da dama fara tserewa daga gidajensu, don tsira daga sharrin wasu miyagu.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun rubuta wasikar kai hari
Wannan ya biyo bayan wata wasiƙar barazana da aka samu, wadda ake zargin 'yan bindiga ne suka rubuta ta, inda suka lashi takobin kai hari domin ɗaukar fansar kisan wani kwamandansu, in ji rahoton Daily Trust.
Wasiƙar dai an gano ta ne a cikin jakar makarantar wani ɗalibi a wata makaranta mai zaman kanta dake Paze, lokacin da wani malami yake duba aikin gida na ɗalibin.
A cikin wasikar, 'yan bindigar sun bayyana cewa za su kai hari Kungaboku da Paze domin rama kisan kwamandansu da dakarun soji na "7 Guards Battalion" suka yi a ranar 7 ga Maris.
Rahoton ya nuna cewa an kashe wa 'yan ta'addar kwamandansu ne a lokacin da aka ceto mutane 19 da aka yi garkuwa da su a yankin Gidan Dogo.
Hare-haren 'yan bindiga a garuruwan Abuja
Yankunan Kungaboku da Paze, waɗanda ke kusa da Byazhin a ƙaramar hukumar Bwari, sun fuskanci tashe-tashen hankula akai-akai a 'yan kwanakin nan:
- Harin ranar 5 ga Maris, 2026: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da wani tsohon soja, Bankole Ganiyu, tare da yara uku. A ranar ne kuma suka kashe wani ɗan banga tare da sace ma'aikatan gona uku.
- Harin ranar 15 ga Maris, 2026: Kwana ɗaya kafin bayyanar wasiƙar barazanar, 'yan bindiga sun kai hari wani matsugunin Fulani a Kungaboku inda suka sace mata uku tare da neman kuɗin fansa har naira miliyan 70.
- Sace mutane 12: Cikin makonni biyu da suka gabata, an sace akalla mutane 12 a yankin Paze, ciki har da yaran wani fasto guda huɗu da matar wani shugaban 'yan banga, in ji rahoton AIT News.
- Kisan Dr. Ifeanyi Ogbu: A watan Oktoban 2025, 'yan bindiga sun kashe tsohon shugaban ƙungiyar likitocin dabbobi na Abuja (NVMA) a Kungaboku bayan sun yi garkuwa da shi tare da yaransa.

Kara karanta wannan
Ana tsaka da yakin Iran da Isra'i'a, bam ya tarwatse a kusa da makarantar yahudawa

Source: Twitter
Matakan da jami'an tsaro suka dauka
Domin kwantar da hankalin mazauna yankin da kuma dakatar da kwararar mutanen da ke barin gidajensu, shugaban 'yan sanda na yankin Byazhin ya gudanar da taron gaggawa a fadar basaraken Kungaboku, Chief Ishaya Jagaba.
A wurin taron, ɗan sandan ya tabbatar da samuwar wasiƙar amma ya ba mazauna yankin tabbacin cewa an ɗauki matakan tsaro masu ƙarfi, in ji rahoton Vanguard.
Babban jami'in ya bukaci mutane su kara sanya ido kan masu sana'ar achaba da masu kwashe gwangwan waɗanda wasu lokutan ke zama masu kai wa 'yan bindiga bayanan sirri.
'Yan bindiga sun sace sarki a Abuja
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun sace Hakimin Dnako, HRH Etsu Yuda Garba, da jikokinsa biyu a birnin tarayya Abuja.
Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa 'yan ta'addar sun sace wasu mutum biyar daga gidaje daban-daban a cikin dare yayin harin.
Mutanen yankin sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi harbi a yankin domin tsoratar da mutane kafin su samu damar tserewa daga wajen.
Asali: Legit.ng
