'Yan Ta'adda Sun Farmaki Sakataren Kungiyar Izala a inda Yake Tafsirin Alkur'ani

'Yan Ta'adda Sun Farmaki Sakataren Kungiyar Izala a inda Yake Tafsirin Alkur'ani

  • Sheikh Abubakar Puma ya tsira daga harin wasu yan ta'adda a Birin Fulani bayan an yi yunkurin kashe shi a masaukin da yake gudanar da tafsiri
  • Kungiyar JIBWIS ta gano Zakariya Muhammad, wanda ya yi barazanar cewa za su dauki matakin kashe malamin, jim kadan kafin a kai harin
  • An samu jinkirin dauki daga yan sanda saboda rashin man fetur a motarsu, kamar yadda babban yaron Sheikh Puma ya shaidawa Legit Hausa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Gombe - Wasu 'yan ta'adda sun kai hari masaukin Sheikh Abubakar Mahmoud Puma, wurin da yake gabatar da tafsirin Alkur'ani a kauyen Birin Fulani, jihar Gombe.

An ruwaito cewa maharan sun farmaki Sheikh Abubakar, wanda shi ne sakataren kungiyar Izala na jihar Gombe a daren jiya Asabar, da yunkurin kashe shi.

Kara karanta wannan

Luguden wutar Amurka da Isra'ila ya yi barna a kasar Musulunci ta Iran, sama da mutum 100 sun mutu

'Yan ta'adda sun farmaki malamin addinin Musulunci a wurin da yake Tafsirin Alkur'ani a Gombe.
Sakataren kungiyar Izala na Gombe, Sheikh Abubakar Mahmoud Puma da 'yan bindiga suka farmaka. Hoto: Kasimu Muhammad
Source: Facebook

An kai hari kan sakataren Izala a Gombe

Wani dan agajin kungiyar Izala, Rabi'u B Goro ya fadi yadda harin ya guna a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa:

"Cikin daren jiya ne wasu matasan 'yan ta'adda suka kai wa sakataren malamai na kungiyar Izala reshen jihar Gombe hari a masaukinsa inda Sheikh Jingir ya tura shi tafsiri cikin garin Biri dake karamar hukumar Nafada.
"Wasu majiyoyi sun bayyana cewa matasan sun kaiwa malamin addinin Musuluncin hari ne da niyyar kai shi lahira, inda suka jikkata wani dan agaji dake bakin aiki a gidan.
"Bayan daukar lokaci ana fafatawa, an samu taimako daga shugaban karamar hukumar Nafada Hon. Babangida Jigawa tare da jami'an sojoji, 'yan sanda da sauran su."

Jibwis ta gano masu shirya harin

Kungiyar Jibwis ta jihar Gombe ta wallafa a shafinta na Facebook cewa sun gano daya daga cikin wadanda suka yi yunkurin kashe babban malamin.

Kara karanta wannan

Hadimin Osinbajo ya raba wa ADC gardama, ya fadi mutum 2 da suka dace da yin takara a 2027

A sanarwar da ta fiyar, kungiyar Jibwis ta ce:

"Wani matashi mai suna Zakariya Muhammad ya rubuta a wani comment da yayi a karkashin hoton Sheikh Abubakar Mahmood Puma cewa za su kashe shi.
"Bayan wasu 'yan awanni kuma sai aka kaddamar da mummunan hari a kan Shehin Malamin a masaukinsa a garin Birin Fulani, inda akayi yunkurin kasheshi, kamar yanda Zakariya ya ambata cewa za su yi.
"Saboda haka muna sanar da jami’an tsaro cewa ga babban wanda ake zargi nan mun samu, wanda na tabbata yana da cikakkiyar masaniya a kan abin da aka shirya, da wadanda suka shirya abin.

Halin da Sheikh Abubakar yake ciki

A zantawar Legit Hausa da Hammad Abubakar Puma, babban d'an shehin malamin, ya shaida cewa:

"To a halin yanzu dai malam yana cikin koshin lafiya, maganar karshe da na yi da shi, jami'an tsaro sun zo tare da shugaban karamar hukumar Nafada, sun dauke shi, bayan wadanda suka kai farmakin sun tare hanya sun ce malam ba zai fita garin ba sai dai in gawarsa.

Kara karanta wannan

Iran ta ji wuta, ta shirya mika wuya ga Amurka? Trump ya yi magana

"Amma da ciyaman da jami'an tsaro suka fita da shi daga garin sun yi Nafada da shi zuwa ofishin 'yan sanda. Maganar da muka yi da shi, ya ce mun su 'yan sandan suna daukar bayanansa. Bayan sun kama ya ce mun suna hanyar dawowa gidansa da ke cikin garin Kumo."
Sakataren kungiyar Izala na Gombe ya tsallake rijiya da baya da 'yan ta'adda suka yi yunkurin kashe shi.
Taswirar jihar Gombe, inda aka yi yunkurin kashe sakataren kungiyar Izala. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jinkirin zuwan 'yan sanda ceto Sheikh

Hammad Abubakar, ya kuma shaida wa Legit Hausa cewa ya samu lambobin DPO na Nafada da kuma DCO, wadanda ya kira don sanar da su halin da mahaifinsa yake ciki, sun kuma tabbatar masa sun samu kiran gaggawa, sannan suna shirin kai dauki.

Sai dai, bayan mintuna kusan 20 da kiransu, ya sake yin magana da su, inda suka shaida masa cewa motarsu ce babu mai, amma suna kokarin samun man fetur din don kama hanyar Birin Fulani.

"Dukkansu sun ce sun riga sun samu kiran gaggawa tun kafin ma ni na kira, cewa suna shirin za su je su kai agajin gaggawa. Bayan nan, zuwa kamar mintuna 20, sai na kara samun labarin cewa wadanda suka kai harin suna nan suna cin karensu ba babbaka, suna ji wa junansu rauni da su da 'yan agajin da ke tsaron gidan malam.
"To sai na kira ('yan sandan) don jin abin da ke faruwa, suka ce mun lallai babu mai ne a cikin motar tasu. Suka ce dai suna kokarin su nemo su sanya a motar su taho.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta cafke mai martaba sarki, ana zargin ya yi sama da faɗi da N250m

"To, na ci gaba da kiransu dai a kai a kai, duk in na kira suna ce mun babu mai a motarsu, magana daya suke fada, har zuwa bayan sallar Asuba, kafin nan na samu tabbacin cewa lallai jami'an tsaron sun riga sun iso wurin, amma tun kafin su isa wurin, gari ya fara waye wa, mutanen garin sun bada kariya, tarzomar ta lafa."

- Hammad Abubakar Puma.

'Yan ta'adda sun farmaki limamin Izala

A wani labari, mun ruwaito cewa, ’yan bindiga ne sun kai mummunan hari gidan Limamin JIBWIS, Imam Abubakar Muhammad Digare, inda suka yi garkuwa da iyalansa.

Rahotanni sun ce maharan sun kutsa gidan cikin dare, suka kwashe matansa da ’ya’yansa zuwa wurin da ba a sani ba, lamarin ya girgiza al’umma.

An kai harin ne a garin Digare, gundumar Gwana, karamar hukumar Alkaleri ta jihar Bauchi, inda jama’a ke nuna damuwa kan matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com