Iran Ta Harba Makaman Roka Makwabta, Mutane 140 Sun Raunata har da Ƴan Najeriya

Iran Ta Harba Makaman Roka Makwabta, Mutane 140 Sun Raunata har da Ƴan Najeriya

  • Kasar Iran ta harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa
  • Wannan lamarin ya jikkata mutane sama da 140 ciki har da ‘yan Najeriya wanda ya tayar da hankali matuka
  • Harin ya tayar da hankalin dubban ‘yan Najeriya mazauna UAE, yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara tsananta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - A ci gaba da yaki da ake yi, kasar Iran ta harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.

Lamarin ya jawo sanadin raunata mutane sama da 140 suka jikkata, ciki har da ‘yan Najeriya da ke aiki a can.

Harin Iran ya taba yan Najeriya a UAE
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Ma’aikatar tsaron UAE ta bayyana cewa tsarin kariyar sararin samansu ya dakile wasu makamai tara da jirage marasa matuki 33 da aka harba ranar 14 ga Maris, 2026, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Da gaske Netanyahu ya bata yayin yakin Isra'ila da Iran? An samu bayanai

Yan Najeriya sun samu rauni a harin Iran

A cewar ma’aikatar, harin ya yi sanadin mutuwar mutane shida tare da jikkata wasu 141 daga kasashe daban-daban ciki har da mazauna kasashen waje.

Rahotanni sun ce daga cikin wadanda suka mutu akwai ‘yan UAE da kuma baki daga Pakistan, Nepal da Bangladesh.

Sai dai hukumomi ba su bayyana ainihin wuraren da aka samu wadanda suka mutu ko suka jikkata ba a sassan kasar.

An ce daga cikin wadanda suka jikkata akwai mutane daga kasashe da dama ciki har da Najeriya, Masar, Sudan, Habasha da kuma Philippines.

Sauran kasashen da aka ambata sun hada da Pakistan, Iran, India, Bangladesh, Sri Lanka da kuma wasu kasashe na Gabas ta Tsakiya.

Lamarin ya tayar da damuwa a tsakanin al’ummar ‘yan Najeriya da ke zaune a UAE, inda dubban mutane ke aiki a fannoni kamar gine-gine da kasuwanci.

Yan Najeriya sun samu raunuka a harin Iran
Marigayi Ali Khamenei, Bola Tinubu da Benjamin Netanyahu. Hoto: @khamenei_ir, Bayo Onanuga, Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Hukumar kula da yan Najeriya ta magantu

Bayanan hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje sun nuna cewa UAE na daya daga cikin manyan wuraren da ‘yan Najeriya ke zuwa aiki a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Tsautsayi ya gitta, harin kasar Iran ya rutsa da 'dan Najeriya da wasu mutane sama da 100

Birane kamar Dubai, Abu Dhabi da Sharjah na daukar dimbin ‘yan Najeriya masu aiki a fannoni daban-daban na tattalin arziki.

Gwamnatin Najeriya ta taba nuna damuwa kan lafiyar ‘yan kasarta a UAE sakamakon takaddamar diflomasiyya da takunkumin biza da aka taba kakabawa ‘yan Najeriya.

Ma’aikatar tsaron UAE ta ce kasar na cikin shiri domin tinkarar duk wata barazana da za ta iya kawo cikas ga tsaron kasa.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na yankin sun nuna cewa hare-haren wani bangare ne na karuwar rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Tashar Al Jazeera ta ce Iran na ci gaba da kai hare-haren makamai masu linzami da jiragen marasa matuki duk da korafe-korafen kasashen makwabta.

Netanyahu ya kalubalanci Mojtaba Khamenei

Kun ji cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ba zai iya fitowa bainar jama’a ba.

Netanyahu ya ce Amurka da Isra'ila na “murkushe” gwamnatin Iran da kungiyar Hezbollah da aka fa tun a farkon shekarun 1980s.

Mojtaba Khamenei ya ce Iran za ta ci gaba da kai hari kan sansanonin sojojin kasar Amurka a yankin gabas ta tsakiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.