'Yan Najeriya na Kukan Tsadar Litar Mai, Tinubu Ya Kafa Kwamiti kan Man Fetur

'Yan Najeriya na Kukan Tsadar Litar Mai, Tinubu Ya Kafa Kwamiti kan Man Fetur

  • Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Fola Adeola a matsayin shugaban kwamitin garambawul ga fannin man fetur domin samar da dabarun bunƙasa tattalin arziki
  • Kwamitin na da alhakin samar da hanyoyin jawo jarin dala biliyan 10 cikin gaggawa da kuma tsara fasalin makamashi na shekaru 10 masu zuwa
  • Shugaban ya umarci dukkan hukumomin gwamnati su ba kwamitin goyon baya tare da mika takardun bincike domin tabbatar da nasarar wannan shiri

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa wani kwamitin bincike da fasalta fannin man fetur na ƙasa domin samar da sabbin sauye-sauye a fannin.

Shugaban ya naɗa Mista Fola Adeola, fitaccen masanin harkar kuɗi kuma wanda ya kafa bankin GTB, a matsayin shugaban wannan kwamiti na musamman.

Shugaba Bola Tinubu ya nada kwamiti kan gyaran fannin man fetur
Shugaba Bola Tinubu ya na rattaba hannu kan wata takarda. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya nada kwamitin gyaran fannin fetur

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya waiwayi mata, ya shirya tsamo miliyoyi daga kangin talauci

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da kafa kwamitin a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

Bayo Onanuga ya bayyana cewa wannan kwamiti zai yi aiki ne ba tare da tsoma bakin kowa ba domin samar da tsare-tsaren da za a iya aiwatarwa cikin gaggawa.

Kwamitin ya ƙunshi kwararru kamar Ademola Adeyemi-Bero da Osagie Okunbor, waɗanda aka ɗora wa alhakin maida fannin man fetur na Najeriya ya zama mai gaskiya da kuma janyo hankalin masu zuba jari.

Babban burin wannan kwamiti shi ne buɗe hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma ƙarfafa matsayin Najeriya a fannin makamashi na duniya.

Manyan ayyuka 3 da aka dora wa kwamitin

Shugaba Tinubu ya umarci kwamitin da ya samar da muhimman tsare-tsare guda uku cikin watanni shida kafin a rushe shi:

  • Tsarin gyara na gaggawa: Samar da dabarun gyaran dokoki da tsarin hukumomi domin magance matsalolin da suka dabaibaye fannin man fetur.
  • Tsarin haɓaka jari: Gano hanyoyin da za su kawo jari na dala biliyan 5 zuwa biliyan 10 cikin sauri ba tare da shafar moriyar ƙasa ba.
  • Tsarin makamashi na shekaru 10: Samar da dogon taswirar aiki mai ƙunshe da ma'aunan yawan man da ake hako da kuma gudunmawar fannin ga tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Bayan harin Boko Haram da ya girgiza sojoji, Tinubu ya canza taku game da tsaro

Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin gyaran fannin man fetur na Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu yayin da za a fara taron majalisar zartarwa a Abuja. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Umarnin Tinubu ga ma'aikatun gwamnati

Shugaban ya kuma umarci dukkan ma'aikatu da hukumomin gwamnati da su ba kwamitin cikakken goyon baya ta hanyar samar da duk wasu bayanai da takardun da suke buƙata.

Wannan mataki na nuna yunƙurin gwamnatin Tinubu na tabbatar da cewa fannin man fetur ya zama ginshiƙin da zai dore wajen haɓaka tattalin arzikin Najeriya da kuma samar da ayyukan yi.

Karanta sanarwar Onanuga a nan kasa:

Farashin litar man fetur a Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, matatar Dangote ta tausayawa 'yan Najeriya, ta rage farashin fetur da dizal yayin da yakin Iran da Amurka ya jawo tsadarsa.

Hakan na zuwa ne bayan rahotanni sun nuna cewa gangar danyen mai ta sauka a karon farko a kasuwar duniya bayan fara yakin Gabas ta Tsakiya a karshen watan Fabrairu, 2026.

Bisa ga sabon jadawalin farashin da matatar ta fitar a ranar 10 ga Maris, 2026, an rage farashin man fetur daga N1,175 zuwa N1,075 kan kowace lita a wurin bada sari ga 'yan kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com