Rai Bakon Duniya: Ɗan Wasan Kannywood Ya Riga Mu Gidan Gaskiya ana cikin Azumi
- Shahararren jarumin fina-finan Hausa wanda ya yi tashe a cikin shirin Garwashi ya rasu a Kano bayan jinya
- Rahotanni sun ce marigayin ya rasu ne a asibitin Malam Aminu Kano bayan ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya kafin mutuwarsa
- Ana shirin gudanar da jana'izarsa yanzu haka a Masallacin Al-Masjlisul Islami da ke Hotoro kusa da Gidan Man Gade-Gade a Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Shahararren jarumin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Umar Ascon, ya riga mu gidan gaskiya a Kano.
Marigayin wanda mutane da dama suka fi sani da Alhaji Lado Mai Barkono a shirin Garwashi ya rasu.

Source: Facebook
An yi rashin dan wasan Kannywood a Kano
Rahotanni daga TRT Hausa sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a asibitin Malam Aminu Kano.
An tabbatar da mutuwar marigayin ne bayan ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya mai tsanani wanda ya yi sanadiyar rasa ransa daga baya.
Mutuwar jarumin ta jefa masoyansa, abokan aikinsa da kuma masu kallon shirin Garwashi cikin alhini, musamman waɗanda suka saba ganin rawar da yake takawa.
An ce ana shirin gudanar da sallar jana’izar marigayin a Masallacin Al-Masjlisul Islami da ke Hotoro 'Ring Road' kusa da Gidan Man Gade-Gade a Kano.
Masoya da abokan arziki na ci gaba da aika sakonnin ta’aziyya tare da addu’ar Allah ya gafarta masa, ya jikansa da rahama, ya sa Aljanna ta zama makomarsa.
Mutane da dama sun yaba da gudunmawar da marigayin ya bayar a masana'antar Kannywood wanda ba za a mance da ita ba.

Source: Facebook
Lawan Ahmad ya yi jimamin mutuwar Umar Ascon
Abokin aikinsa a masana'antar Kannywood, Lawan Ahmad ya nuna jimaminsa game da rasuwar marigayin a yau Asabar 14 ga watan Maris, 2026.
Lawan ya bayyana haka ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na Facebook a yammacin yau Asabar 14 ga watan Maris, 2026.
Ya ce:
"Inna lillahi wa inna ilayhi raji'un.
" Allah yayi wa Umar Ascon (Tajo) a cikin shirin Laure rasuwa yanzu nan, muna barar addu'ar ku Allah ya sa mutuwa hutu ne a gare shi."
Mutane da dama sun yi martani a sashen sharhi bayan wallafa rasuwar marigayin da Lawan Ahmad ya yi.
Mafi yawansu sun nuna jimami tare da yi masa addu'o'in samun rahama a gobe kiyama da kuma ba iyalansa hakurin jure wannan babban rashi da aka yi.
Mai shirya fina-finai a Kannywood ya rasu
A baya, mun ba ku labarin cewa masana'antar Kannywood ta shiga jimami sakamakon rasuwar babban mai shirya fim, Nura Sharif kuma na hannun daman Abdul Amart.
Abdul Amart Maikwashewa ya siffanta marigayin a matsayin mutumin kirki mai hakuri da dattako wanda ya rasu yana shirin tafiya Umra.
Hamisu Lamido Iyantama ya bayyana cewa marigayi Nura Sharu ya dade a masana'antar tun zamanin 'Linear' kafin zuwan kwamfuta wanda ya ba da gudunmawa sosai
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

