Ministan Tsaro Ya Faɗi Dalilin da Ya Sa Ƴan Ta'adda Suka fi Kai Hare Hare a Ramadan

Ministan Tsaro Ya Faɗi Dalilin da Ya Sa Ƴan Ta'adda Suka fi Kai Hare Hare a Ramadan

  • Rundunar sojojin Najeriya ta roƙi ‘yan ƙasa kada su karaya game da ikon dakarunsu a wajen fatattakar miyagun ‘yan ta’adda
  • Ministan tsaro ya ce duk da hare-haren ‘yan ta’adda a wasu wurare kamar Ngoshe a Gwoza, sojoji sun kashe kwamandojinsu tare da lalata sansanoninsu
  • Ya ƙara da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da sababbin makamai da kayan aiki, yana mai jaddada cewa rundunar tsaro ta inganta dabarun yaƙi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya roƙi ‘yan Najeriya su ba da hadin kai game da yaki da ta'addanci.

Minista C.G Musa ya roke su da kada su cire tsammani kan ikon rundunar sojin ƙasar wajen murƙushe ‘yan ta’adda.

Ministan tsaron Najeriya ya roki yan kasa kan yaki da ta'addanci
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Ministan ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa ta sirri da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Lauya ya kitsawa gwamnatin Tinubu yadda za ta tursasa wa Trump kawo karshen yaki da Iran

Minista ya ba Bola Tinubu rahoton tsaro

Musa ya jagoranci shugabannin tsaro domin ba shugaban Najeriyan rahoto duba da yawan hare-haren da ake kai wa a Ramadan.

Ganawar ta mayar da hankali kan yadda yaƙi da ta’addanci ke tafiya, tare da bayyana sababbin matakan da rundunar tsaro ke ɗauka domin ƙara matsa wa ‘yan ta’adda.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mata da yara 100 aka sace a karshen makon da ya gabata bayan ‘yan ta’adda sun kai hari a ƙauyen Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza.

An ce mayakan Boko Haram da na ISWAP sun kai harin ne a hade, inda suka kwace wani sansanin soja kafin su afkawa al’umma da sansanin ‘yan gudun hijira.

Ministan tsaron ya jaddada cewa duk da irin wadannan hare-hare, ‘yan ta’adda na samun mummunar asara yayin da kwamandojinsu da dama ke hallaka a hare-haren sojoji.

Ya amince cewa rundunar soji ma ta yi asarar wasu jaruman jami’ai da sojoji, amma ya ce sadaukarwar da suke yi na nuna kudirin kare ƙasar, cewar Sahara Reporters.

Kara karanta wannan

Bayan harin Boko Haram da ya girgiza sojoji, Tinubu ya canza taku game da tsaro

Ya ce:

“Muna roƙon ‘yan Najeriya kada su gaji ko su karaya, domin idan ana jin wasu labarai sai a ɗauka kamar haka kawai ake ciki.”
Sojoji sun bukaci hadin kan yan Najeriya kan tsaro
Hafsan sojojin Najeriya, Waidi Shaibu da dakarunsa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Alkawarin da Tinubu ya yi kan tsaro

Musa ya ƙara da cewa shugaban ƙasa ya yi alkawarin samar da sababbin makamai da kayan aiki domin ƙarfafa rundunar soji wajen kare ƙasar daga barazanar ‘yan ta’adda.

A cewarsa, rundunar tsaro ta riga ta daidaita dabarunta na yaƙi, kuma a kwanakin baya sojoji sun sake kwato wurare tare da lalata kayan ‘yan ta’adda.

Ya kuma bayyana cewa ana samun ƙarin nasarori a fagen daga, yana mai tabbatar da cewa rundunar tsaro na aiki tare kuma za ta yi nasara.

'Dalilin zuwan sojojin Amurka cikin Najeriya

Mun ba ku labarin cewa Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) ya yi karin haske game da rawar da sojojin Amurka za su taka a kasar nan

Kara karanta wannan

Najeriya ta kai wa mutanenta da suka makale a yaƙin ƙasar Iran agaji

Christopher Musa ya yi bayani ne a wani taron tsaro da aka gudanar a birnin tarayya Abuja da ya samu halartar manyan jami'an gwamnati.

Bayanin ministan ya zo ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke cigaba da tambayoyi game da zuwan sojojin Amurka da saukarsu a Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.