Yadda Yakin Iran da Isra'ila Zai Amfani Najeriya da Tattalin Arzikinta
- Sanata Jimoh Ibrahim ya yi magana kan yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya tsakanin Iran da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka
- Sanatan ya ce rikicin Gabas ta Tsakiya na iya zama dama ga Najeriya saboda karin kudin man fetur zai iya karfafa Naira tare da rage karbar bashi
- Sanatan ya kuma yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda gwamnatinsa ke tafiyar da bashi, yana cewa halin tattalin arzikin kasar na kara inganta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sanatan Ondo ta Kudu, Jimoh Ibrahim, ya ce rikicin Gabas ta Tsakiya na iya kawo babbar dama ga tattalin arzikin Najeriya.
Sanatan ta ce hakan zai samu ne ta hanyar karin kudin man fetur da ake sayarwa da karfafa Naira wanda zai inganta tattalin arzikin kasar.

Source: Getty Images
Sanata ya gano amfanin yakin Iran/Isra'ila ga Najeriya
Sanata Jimoh ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV inda ya yi bayani kan tasirin rikicin yankin ga kasuwar mai da makamashi.
Sanatan ya ce idan farashin mai ya karu, Najeriya za ta samu karin daloli, wanda zai taimaka wurin rage karbar bashi da kuma karfafa darajar kudin Naira.
Ya kara da cewa karin shigar daloli zai bai wa Babban Bankin Najeriya damar shiga kasuwar canji ta bayan fage domin daidaita farashin kudaden kasashen waje.
A cewarsa, idan hakan ta faru, zai taimaka wajen daidaita farashi a kasuwa, wanda hakan zai kara inganta tattalin arziki mai dorewa a Najeriya baki daya.

Source: Twitter
Basuka: An yaba wa Shugaba Bola Tinubu
Sanatan ya kuma yaba wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya kira ci gaba mai kyau a bangaren kula da bashin Najeriya.

Kara karanta wannan
Iran ta fadi sharadin tsagaita wuta kan Amurka, Isra'ila bayan kuskuren farmakinta
Ya ce kafin zuwan Tinubu, kusan kashi 96 cikin 100 na kudin shiga na gwamnati na tafiya wajen biyan bashi, amma yanzu an samu sauki sosai.
A cewarsa, a yanzu rabon kudin shiga da ake kashewa wajen biyan bashi ya ragu zuwa kusan kashi 68 cikin 100 wanda hakan zai taimaka wurin inganta tattalin arziki.
Illar da rikicin zai iya yi ga Najeriya
Sai dai ya amince cewa rikicin na iya haifar da karin kudin man fetur a cikin gida, wanda zai iya kara tsadar sufuri da kuma matsin rayuwa.
Duk da haka, ya nuna kwarin gwiwa cewa gwamnati za ta iya magance irin wadannan kalubale saboda karin kudin shiga daga sayar da danyen mai.
Gwamnatin Tinubu ta magantu kan kayyade farashin fetur
An ji cewa gwamnatin tarayya ta yi ƙarin haske kan farashin man fetur a Najeriya yayin da ake yaki a Gabas ta Tsakiya tun karshen Fubrairun 2026.
Ta ce ba za ta saka hannu wajen kayyade farashin fetur ba duk da tashin hankali a yankin da ya jawo sauye-sauyen farashin mai.
Ministan kudi Wale Edun ya ce gwamnati za ta bullo da wasu matakai domin rage nauyin tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya.
Asali: Legit.ng

