Amurka Ta Kira Ruwa; Kasar Iran Ta Sha Sabon Alwashi a Yakin da Ake Yi

Amurka Ta Kira Ruwa; Kasar Iran Ta Sha Sabon Alwashi a Yakin da Ake Yi

  • A kwanakin baya ne dai babban jirgin ruwan yakin Amurka da ke tafiya a karkashin ruwa ya nutsar da wani jirgin ruwan yakin Iran a cikin teku
  • Nutsar da jirgin ruwan mai dauke da ma'aikata 180 ya jawo an samu asarar rayukan wasu sojojin ruwa na Iran da ke cikinsa
  • Babban kwamandan rundunar sojojin Iran, Amir Hatami, ya yi gargadin cewa ba za su kyale danyen aikin na kasar Amurka ya tafi a banza ba

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tehran, Iran - Babban kwamandan rundunar sojojin Iran, Amir Hatami, ya aika da narko a sanadiyyar nutsar da jirgin ruwa Iran, IRS Dena, da Amurka ta yi a teku.

Amir Hatani ya yi gargadin cewa kisan ma'aikata 104 na jirgin ruwan yaƙin IRIS Dena, ɗaya daga cikin sababbin jiragen yaƙin ƙasar, a Tekun Indiya, ba zai tafi hakanan a banza ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ana cikin gwabza fada, Trump ya fadi bukatar da shugabannin Iran suka nema

Iran ta sha alwashi kan Amurka
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Andrew Cabellero-Reynolds, Reza B
Source: Getty Images

Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa babban kwamandan rundunar sojojin ya bayyana cewa za su dauki fansar nutsar da jirgin ruwan yakin.

Amurka ta nutsar da jirgin ruwan yakin Iran

Wani babban jirgin ruwan yakin Amurka wanda ke tafiya a karkashin ruwa ne dai ya nutsar da jirgin ruwan na Iran a kusa da gabar tekun kasar Sri Lanka a ranar, 4 ga watan Maris 2026.

An nutsar da jirgin ruwan ne yayin da yake dawowa daga atisayen sojoji a kasar Indiya bayan amsa gayyatar da aka yi masu.

Kasar Iran za ta dauki fansa kan Amurka

Amir Hatami ya bayyana cewa sojojin da ke cikin jirgin an farmake su ne yayin da suke kan hanyar komawa gida.

“Ma’aikatan jirgin ruwa na Dena sun kammala wani aiki na zaman lafiya ne kuma an farmake su da hari yayin da suke kan hanyarsu ta komawa Iran."

- Amir Hatami

Kara karanta wannan

Iran ta shiga matsala: Bataliyar sojojin Amurka mai hatsari ta bar Japan zuwa Gabas

Iran ta ce sojojin ruwan sun kafa tarihi

Hatami ya kuma ƙara da cewa an kai wa sojojin ruwan hari ne duk da cewa ba sa tsaka da wata fafatawa ta kai-tsaye.

"Sunan Dena da sadaukarwar ma'aikatansa za su kasance alamar juriya da sadaukarwa a tarihin rundunar sojojin ruwa ta Iran.

- Amir Hatami

Ya ci gaba da jaddada ƙudurin Iran, inda ya ƙara da cewa:

"Rundunar sojoji za ta kare iyakokin ruwa na Iran kuma za ta ƙarfafa ikon rundunar sojin ruwanta da ma fiye da baya."

An mika gawawwakin sojojin ga Iran

Wannan matsayi ya ƙara samun ƙarfi a ranar Juma'a lokacin da gwamnatin Iran ta fitar da hotunan akwatunan gawarwakin sojojin ruwa na IRIS Dena da suka mutu.

A wani saƙo da ta wallafa a shafin X, ofishin jakadancin Iran da ke Indiya ya bayyana cewa:

"Gawawwaki masu tsarki da daraja na shahidan sojojin ruwa waɗanda suka rasa rayukansu a harin ta'addanci da dakarun Amurka suka kai wa jirgin ruwan yaƙin IRIS Dena."

Kara karanta wannan

Birtaniya ta fasa ƙwai, ta faɗi ƙasar da ke taimakawa Iran a yaƙi da Amurka

Iran ta sha alwashin ramuwar gayya kan Amurka
Ministan harkokin wajen kasar Iran, Seyed Abbas Araghchi Hoto: @araghchi
Source: Twitter

Sojojin Iran sun lalata jiragen Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami kan wani sansanin sojojin Amurka da ke kasar Saudiyya.

​Hare-haren na makamai masu linzami sun latata wasu jiragen da Amurka ke amfani da su a Gabas ta Tsakiya.

An lalata jiragen da ke dakon mai na rundunar sojin saman Amurka guda biyar yayin da suke sansanin soji na Prince Sultan da ke Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng