Birtaniya Ta Fasa Ƙwai, Ta Faɗi Ƙasar da Ke Taimakawa Iran a Yaƙi da Amurka
- Ministan tsaron Biritaniya ya bayyana cewa Rasha na marawa Iran baya wajen amfani da jirage marasa matuka domin yakar Amurka da Isra'ila
- John Healey ya yi ikirarin cewa Rasha na tura wa Iran dabarun yaki da ta koya a yakinta da Ukraine domin rura wutar rikicin Gabas ta Tsakiya
- Wannan na zuwa ne yayi da Biritaniya ta kakkabo wasu jiragen Iran dake kokarin kai hari sansanonin soji yayin da yakin yake cigaba da tsananta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Birtaniya - Ministan Tsaron kasar Biritaniya, John Healey, ya bayyana cewa akwai alamun shugaban Rasha Vladimir Putin ya na taimakawa Iran a yakin da take yi da Amurka da Isra'ila.
John Healey ya ce dukkan alamu sun nuna cewa Iran na samun taimakon Rasha a hare-haren jirage marasa matuka da take kai wa dakarun Amurka da na Isra'ila a Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Birtaniya na zargin Rasha na taimakawa Iran
Ministan tsaron ya bayyana hakan ne yayin da yake ziyartar hedkwatar sojojin Biritaniya dake Northwood, kamar yadda rahoton Sky News ya nuna.
John Healey ya jaddada cewa Rasha na amfani da dabarun da ta koya a yakin Ukraine domin karfafa wa Iran gwiwa a wannan sabon rikicin da ya barke tun ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
A cewar Ministan, kwararrun sojoji suna gudanar da bincike na tsanaki kan wani jirgi marar matuki kirar Iran wanda ya daki sansanin sojin saman Biritaniya na Akrotiri dake kasar Cyprus a ranar 1 ga Maris, 2026.
Manufar binciken ita ce gano ko akwai sassan na'urori ko fasaha daga kasar Rasha a cikin jirgin.
Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun nuna cewa Iran ta sayar wa Rasha dubban jiragen "Shahed" a farkon yakin Ukraine, kuma yanzu Rasha na mayar a biki ta hanyar ba Iran sababbin dabarun yaki.

Kara karanta wannan
Iran ta fadi sharadin tsagaita wuta kan Amurka, Isra'ila bayan kuskuren farmakinta
Alaka tsakanin Rasha da Iran
Masana harkokin sojoji na Biritaniya sun bayyana cewa akwai tabbatattun alamun alaka tsakanin Moscow da Tehran, musamman yadda Iran take amfani da jirage marasa matuka yadda Rasha take yi.
Minista Healey ya nuna cewa Putin ne kadai shugaban duniya da yake amfana da tashin farashin mai sakamakon wannan yaki, wanda hakan ke ba shi kwarin gwiwar rura wutar rikicin.
Duk da cewa Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ba shi da tabbataccen bayanin cewa Rasha na goyon bayan Iran, Biritaniya ta dage cewa hadin gwiwar kasashen biyu na barazana ga tsaron yankin, in ji rahoton The Guardian.

Source: Getty Images
Sojojin Birtaniya sun kakkabo jiragen Iran
A wani bangaren kuma, sojojin Biritaniya dake sansanin Erbil a kasar Iraki sun bayar da rahoton cewa sun taimaka wajen kakkabo wasu jirage marasa matuka na Iran guda biyu a ranar Laraba.
Ko da yake harin da aka kai sansanin Akrotiri bai jikkata kowa ba, ya nuna yadda karfin makaman Iran yake karuwa cikin sauri.

Kara karanta wannan
Amurka da Isra'ila sun sha mamaki, an gano abin da Iran ke amfani da shi a musayar wuta
Wannan hadin gwiwa tsakanin Rasha da Iran na kara dagula lissafin sojojin Amurka da na Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rasha ta fi amfana da yakin Iran
Tun da fari, kun ji cewa, shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Antonio Costa, ya ce har zuwa yanzu Rasha ce kadai ke cin gajiyar yakin da kasashen Amurka da Isra'ila ke yi da Iran.
Da yake magana kan yakin, Costa ya ce tashin farashin mai sakamakon rikicin na ba Rasha karin kudaden shiga da za ta iya amfani da su wajen daukar nauyin yakin da take yi da Ukraine.
A cewar Costa, farashin mai da ya karu ya samar wa Rasha karin kudaden shiga, sannan kuma Amurka ta karkatar da wasu makamai da za a iya turawa Ukraine.
Asali: Legit.ng
