Ana Batun Yakin Iran, an Bayyana Hadarin da Ya Tunkaro Kano da Wasu Jihohin Arewa 10

Ana Batun Yakin Iran, an Bayyana Hadarin da Ya Tunkaro Kano da Wasu Jihohin Arewa 10

  • Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da sanarwar gargadi kan abin da yake tunkaro wasu jihohin Arewa
  • NiMet ta bayyana cewa akwai yiwuwar samun barkewar cutar sankarau a wasu jihohin Arewa saboda yanayi na zafi da kura
  • Hukumar ta ba da shawarar mutane da su guji wurare masu cunkoso da kula da tsafta domin kaucewa kamuwa da cutar

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa jihohin Arewa da dama suna fuskantar babban haɗarin kamuwa da cutar sankarau.

Hukumar NiMet ta tarayya ta yi gargadin ne yayin da yanayin zafi da ƙura ke ci gaba da addabar yankin.

Hukumar NiMet ta yi gargadin barkewar cutar sankarau a jihohin Arewacin Najeriya
Ma'aikatan lafiya na yin allurar cutar sankarau Hoto: Issouf Sanogo
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar gargaɗi kan haɗarin cutar sankarau da hukumar NiMet ta fitar ranar Alhamis, 12 ga watan Maris, 2026 a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Lauya ya kitsawa gwamnatin Tinubu yadda za ta tursasa wa Trump kawo karshen yaki da Iran

Cutar sankarau na iya yaduwa cikin sauri

Hukumar ta ce cutar na iya yaɗuwa cikin sauri kuma tana iya yin kisa a cikin sa'o'i kaɗan idan ba a yi maganinta da wuri ba.

Bisa taswirar sa ido na hukumar na watan Maris 2026, jihohi 11 ne suka faɗa ƙarƙashin rukunin masu babban haɗari.

Wadanne jihohin Arewa aka lissafo?

Jihohin da abin zai shafa sun haɗa da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina, Kano, Jigawa, Adamawa, Gombe, Bauchi, Yobe da kuma Borno.

NiMet ta lura cewa yanayin muhalli kamar ƙura da yanayin zafi a halin yanzu suna taimakawa wajen ɓulla da yaɗuwar cutar a waɗannan yankuna.

Duka wadannan jihohi suna yankin Arewa maso gabas da kuma Arewa maso yammacin Najeriya ne.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Cutar na iya tsananta cikin sauri kuma tana iya zama barazana ga rayuwa a cikin sa'o'i kaɗan idan ba a yi magani ba. To sai dai kuma, gano cutar da wuri da kuma gaggauta ba da maganin kariya na taimakawa ƙwarai wajen rayuwa da rage matsaloli."

Kara karanta wannan

Magana ta Fito: Barnar da bama baman Iran suka yi wa sojojin Amurka bayan kai hari

An shawarci mazauna yankunan tsakiyar ƙasar nan da su kasance cikin shiri tare da bayar da rahoton duk wata alama da ake zargi da wuri.

Hukumar ta kuma lissafa Plateau, Oyo, Cross River, Edo, Ekiti da Enugu a cikin jihohin da ke da ƙananan matakan gargaɗi.

Nimet ta yi gargadin samun cutar sankarau a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wadanne mutane ne za su iya kamuwa?

NiMet ta ce yara, matasa da mutanen da ke zaune a wuraren da ake cunkoso su ne suka fi fuskantar haɗarin kamuwa da cutar.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

"Mutanen da ke yawan zama a wurare masu rashin ruwa da ƙura, da kuma mutanen da garkuwar jikinsu ta yi rauni, su ma suna cikin haɗari na musamman."

Domin rage haɗarin kamuwa da cutar, hukumar ta buƙaci 'yan Najeriya da su ɗauki matakan kariya kamar yin riga-kafi, kiyaye tsafta mai kyau da kuma guje wa wuraren da ake cunkoso.

Hukumar NiMet ta yi hasashe

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi hasashen samun ruwan sama.

Hukumar NiMet ta yi hasashen samun ruwan sama zai sauka da wuri a Kano, Neja, Rivers da wasu jihohi 12.

Rahoton hukumar ya nuna cewa za a samu karancin ruwan sama a jihohin Katsina da Zamfara idan aka kwatanta da yadda aka saba gani a shekarun baya da suka wuce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng