An Fara Kiran Tinubu Ya Ajiye Amurka a Gefe, Ya Dauki Darasi daga Kasar Iran
- Lauya mai rajin kare hakkin dan Adam, Femi Falana SAN ya bayyana cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta dauki darasi daga kasar Iran
- Femi Falana ya bayyana cewa Amurka ba za ta taba daidaita lamura a Najeriya ba, inda ya yi kira ga hukumomi su tashi su gyara kasar
- Ya yi magana ne a daidai lokacin da Iran ke cigaba da harba makamai kan kadarorin Amurka da Isra'ila a Gabas ta Tsakiya bayan fara yaki
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fitaccen lauya mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta sake tsara tsarin kasar tare da karfafa kayan aiki da horo ga rundunar sojoji da ‘yan sanda.
Femi Falana (SAN) ya yi magana yana mai gargadin cewa dogaro da kasashen waje kamar Amurka ba zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya ba.

Kara karanta wannan
Iran ta fadi sharadin tsagaita wuta kan Amurka, Isra'ila bayan kuskuren farmakinta

Source: Getty Images
Falana ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a Channels Television, inda ya ce dole shugabannin Najeriya su tashi tsaye.
Gargadi kan dogaro da kasar Amurka
Femi Falana ya ce manufofin gwamnatin Amurka karkashin shugaba Donald Trump sun haifar da matsananciyar matsalar jin kai a Cuba, ciki har da karancin mai.
Punch ta rahoto ya ce:
“Shi (Trump) ya haifar da matsalar jin kai a Cuba. Ba a kai musu mai, kuma ka san abin da hakan ke nufi idan aka kwatanta da halin da Najeriya take ciki. Wannan ne ya sa dole Najeriya ta farka.”
Falana ya bukaci gwamnatin Najeriya ta dauki darasi daga yakin da ke gudana a Iran da kuma rawar da Amurka ke takawa a cikinsa.
Ya ce:
“Dole ne mu koyi darasi daga Iran cewa matukar ba ka sake tsara kasarka ba, matukar ba ka karfafa rundunar sojojinka ba, matukar ba ka inganta rundunar ‘yan sandanka ba,

Kara karanta wannan
Shugaba Edogan ya yi gargadi da ya hango gagarumar matsala a yakin Iran da Amurka
"babu yadda wata kasa mai neman rinjaye kamar Amurka za ta tabbatar da doka da oda a kasarka.”
Batun karuwar ta'addanci a Najeriya
Femi Falana ya yi bayani ne a daidai lokacin da ake samun karuwar hare-haren ‘yan ta’adda a fadin kasar nan duk da tallafin da Amurka ta ce za ta bayar.
Ya ce:
“Tun daga watan Disamban 2025, lokacin da wannan mutum (Trump) ya fada a ranar Kirsimeti cewa, ‘Na kai hari Najeriya na kashe ‘yan ta’adda,’ tun daga lokacin ne ta’addanci ya fara karuwa a kasarmu.”
Falana ya jaddada cewa dole ne gwamnati ta sake nazari domin karfafa cibiyoyin tsaro na Najeriya:
“Shi ya sa dole gwamnatin Najeriya ta sake nazari domin duba yadda za a inganta rundunar sojojinta.”

Source: Facebook
Ana kama masu sukar Isra'ila a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Dr Bashir Aliyu Umar ya yi zargin cewa ana kama masu sukar Isra'ila a Najeriya.
Malamin ya yi korafi da cewa ana kama masu sukar Benjamin Netanyahu a Najeriya a daidai lokacin da ake so a soke dokar hukunta masu zagin Annabi SAW.
Ya kara da cewa kasar Isra'ila ta aikata laifin kisan kare dangi a karkashin jagorancin Benjamin Netanyahu, kuma sun yi Allah wadai da shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng