Shiri Ya Yi: Dakarun Sojoji Sun Yi Bajinta, Sun Kashe Babban Kwamandan ISWAP

Shiri Ya Yi: Dakarun Sojoji Sun Yi Bajinta, Sun Kashe Babban Kwamandan ISWAP

  • 'Yan ta'addan kungiyar ISWAP sun yi yunkurin kai harin ta'addanci kan dakarun sojojin Najeriya a jihar Yobe
  • Hazikan dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama da 'yan ta'addan inda suka samu nasarar hallaka da dama daga cikinsu
  • A cikin sanarwar da aka fitar, an bayyana cewa har da wani babban kwamanda daga cikin 'yan ta'addan da aka hallaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Yobe - Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun kashe aƙalla mambobi 20 na ƙungiyar Boko Haram/ISWAP, a jihar Yobe.

Daga cikin 'yan ta'addan da aka kashe har da wani kwamanda da aka bayyana matsayin Abu Yusu, Munzir na Dursula a Goniri da ke ƙaramar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Sojoji sun hallaka kwamandan ISWAP
Shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da jami'in yada labarai na rundunar OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba ya fitar a shafin X a ranar Alhamis, 12 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a sun yi wa Amurka raddi, za su fito kan titunan Abuja

Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP

An gudanar da samamen ne yayin jerin hare-hare a yankin Goniri, waɗanda aka fara a daren ranar Litinin, 9 ga Maris 2026, kuma aka ci gaba har zuwa farkon sa'o'in ranar Talata, 10 ga Maris 2026.

Sanarwar ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun yi yunkurin kai hari kan sansanonin sojoji ne da ke ƙarƙashin Sassa na 2 na Operation Hadin Kai (OPHK).

Ya ce dakarun sun yi nasarar dakile yunƙurin ’yan ta’addan, wanda ya haɗa da dabarar kutsa kai daga ƙauyen Goniri da kuma mahadar Ngamdu a wani bayyanannen yunƙuri na kewaye sansanonin sojoji.

Dakarun Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP

Haka kuma ya bayyana cewa wasu dakarun sun samu raunuka yayin fafatawar, amma an kwashe su cikin gaggawa kuma suna cikin yanayi mai kyau a halin yanzu.

“Dakarun da ke sa ido sun mayar da martani cikin sauri da nuna fifikon ƙarfin wuta da dabarun yaƙi, tare da daidaita tsarinsu na kariya yayin da aka tura dakarun kai dauki da na sama."

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi; Yadda 'yan Boko Haram suka kashe kwamandojin sojoji 3 cikin sati 1 a Borno

"An yi wa ’yan ta’addan kaca-kaca kuma aka tilasta musu tserewa cikin rudani, inda suka yi asarar rayuka da dama, ciki har da wani babban kwamanda.”
"Bayan fafatawar, dakarun sun gano gawarwaki da dama, makamai, harsasai, bama-baman da aka haɗa da hannu, da sauran kayayyakin da ’yan ta’addan suka bari yayin da suke tserewa."
"Wasu ayyukan share miyagu da aka ci gaba da yi a yankin Timbuktu Triangle, musamman a kusa da Gwaigomari, sun kai ga gano ƙarin gawarwakin ’yan ta’addan."

- Laftanar Kanar Sani Uba

Sojoji sun kashe 'yan ta'addan ISWAP a Yobe
Taswirar jihar Yobe, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Laftanar Kanal Sani Uba ya jaddada cewa yankin yana nan daram a ƙarƙashin ikon sojoji, kuma dakarun ƙasa da na sama suna ci gaba da gudanar da zafafan ayyukan share tsageru a cikin al’ummomin da ke kewaye don kamo duk wani ɗan ta’adda da ya tsira.

'Yan Boko Haram sun hallaka kwamanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun kashe kwamandan sojojin Najeriya a jihar Borno.

'Yan ta'addan na Boko Haram sun kashe babban kwamandan rundunar (CO) da wasu jami’an sojojin Najeriya.

Maharan sun fatattaki dakarun sojoji daga sansanin, suka ƙona motoci tare da kwashe makamai da albarusai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng