Ana Tunanin Azumi 30, Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa ga Musulman Najeriya

Ana Tunanin Azumi 30, Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa ga Musulman Najeriya

  • Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bukaci musulmi su dage da addu'o'i da sadaka a goman karshe ta watan Ramadan
  • Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta fitar ranar Laraba a jihar Kaduna
  • Sanarwar ta tunatar da daukacin musulmin Najeriya muhimmancin neman daren Lailatul Qadr, wanda Sunnah ta fadi dararen da ake nemansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad III ta ja hankalin musulmai game da goman karshe.

JNI ta yi kira ga daukacin al'ummar Musulmi a fadin Najeriya da su kara kaimi wajen addu'o'i, ayyukan sadaka, da sauran ibadu a cikin kwanaki goma na karshen watan Ramadan.

Sarkin Musulmi.
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

Leadership ta tattaro cewa kungiyar ta fitar da wannan kiran ne a jiya Laraba, cikin wata sanarwa da sakatarenta na kasa, Farfesa Khalid Aliyu, ya sanya wa hannu a Kaduna.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta cafke mai martaba sarki, ana zargin ya yi sama da faɗi da N250m

Wannan na zuwa ne yayin da masana ilimin taurari suka fara hasashen cewa azumin bana zai cika 30 cif kafin a samu damar ganin jinjirin watan karamar sallah.

Sarkin Musulmi ya ja hankali kan Lailatur Khadr

Farfesa Aliyu ya bayyana cewa, karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban JNI na kasa, kungiyar ta lura cewa ranar 20 ga watan Ramadan, ta fado ne a ranar 9 ga watan Maris, 2026.

"Wannan lokaci ne na neman daren daukaka, wato Lailatul Qadr, wanda ake kyautata zatonsa a daya daga cikin dararen mara na karshen watan Ramadan," in ji shi.

Sanarwar ta kara da cewa, a bisa koyarwar Sunnah, ana neman wannan dare ne mai albarka a darare na 21, 23, 25, 27, da kuma na 29, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

JNI ta nuna godiyarta ga Allah (SWT) da Ya ba wa Musulmi damar ganin Ramadan na bana, inda ta yi addu'ar Allah Ya ba su juriya da karfin kammala ragowar kwanakin cikin nasara.

Sakon kungiyar JNI ga musulman Najeriya

Haka zalika, kungiyar ta bukaci Musulmi da su tsananta addu’o’i ga kansu da kuma kasa baki daya, musamman domin ganin karshen matsalolin da ke addabar kasar nan.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta ji ruwan wuta, ta fara karaya a shirin da ta yiwa gwamnatin Musulunci ta Iran

A cewar kungiyar, ya kamata Musulmi su shimfida ayyukan alheri ta hanyar ciyarwa da bayar da sadaka ga matalauta, marayu, gajiyayyu, da nakasassu.

Haka kuma, ta tunatar da muminai game da wajabcin bayar da Zakatul Fitr (Sadaƙar Azumi), wadda ake raba wa mabukata a kwanaki uku na karshen Ramadan, ko kuma da sassafe kafin a fara sallar Idi.

Sarkin Musulmi.
Masu Sallah a filin idi da Mai Alfarama Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

A karshe, kungiyar ta bukaci Musulmi da su yi amfani da ragowar kwanakin Ramadan wajen karanta Alkur'ani, fahimtar ma'anarsa, da kuma yin aiki da koyarwarsa.

Ta yi addu'ar Allah Ya yafe wa Musulmi, Ya karbi azuminsu, sannan ta yi fatan alheri na zagayowar bikin karamar sallah (Eid-el-Fitr) cikin kwanciyar hankali da farin ciki.

Wani musulumi kuma dalibin ilimi, Malam Abdullahi Kabir ya shaidawa Legit Hausa cewa 10 ta karshe a Ramadan tana da tsada sosai, ya kamata mutane su dage matuka.

"Garabasa, ni'ima, rahama da gafarar da ke cikin wadannan kwanaki suna da yawa. Daren Lailatul Qadr na ciki, ya kamata mutane su rage barci su nemi duniya da lahira a wurin mai bayarwa," in ji shi.

Kara karanta wannan

Yaki da Iran ya jawo bakin jini ga Isra'ila, Spain ta dauki mataki kan kasar Yahudawa

Sarkin Musulmi ya gindaya sharuddan Tafsir

A baya, kun ji cewa ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) karkashin jagorancin Sarkin Musulmi ta fitar da ƙa’idoji da sharuddan da dole ne malami ya cika kafin fara tafsirin Alƙur’ani.

JNI ta ce ta ƙaruwar malaman da ke gudanar da tafsiri tare da yin habaici, zage-zage da kokarin raba kan musulmai abin damuwa ne ƙwarai.

A cewarta, kamata ya yi tafsiri ya zama hanya ta ilmantarwa da haɗa kan al’umma, ba hanyar haddasa sabani ba da rikici tsakanin mabiya addinin Islama ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262