'Yan Shi'a Sun Yi wa Amurka Raddi, za Su Fito kan Titunan Abuja
- Kungiyar 'yan Shi'a a Najeriya ta sanar da shirinta na yin gangami a birnin tarayya Abuja kwanaki bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei
- A kwanakin baya dai ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya dakatar da aiki saboda tsoron abin da zai biyo baya yayin zanga-zanga
- 'Yan Shi'a sun yi martani da ke cewa bai kamata Amurka ta rufe ofis ba saboda su, inda suka ce ba su da alaka da ta'addanci ko tarzoma
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) ta 'yan Shi’a ta musanta zargin cewa tana shirin kai hari kan ‘yan Amurka ko cibiyoyinsu a Najeriya.
Kungiyar ta yi bayani ne bayan ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya gargadi 'yan kasarsa da su yi hattara yayin da ake tsammanin zanga-zangar 'yan Shi'a.

Kara karanta wannan
Iran ta sake harba makamai, ta yi wa yahudawa mummunar barna a Isra'ila cikin awanni 24

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiyar 'yan Shi'a ta ce ayyukanta suna gudana cikin lumana da bin doka a tsawon shekaru da suka yi.
'Yan Shi'a za su taru a Abuja
Kungiyar ta kuma sanar da cewa ta sanya ranar Juma’a domin gudanar da bikin ranar Kudus na bana tare da jimamin rasuwar jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Wannan na zuwa ne bayan da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da gargadin tsaro kan yiwuwar barazanar ta’addanci da ka iya shafar cibiyoyin diflomasiyya da makarantu masu alaƙa da Amurka a ƙasar.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja, shugaban dandalin IMN Resource Forum, Farfesa Abdullah Danladi, ya yi watsi da zargin cewa kungiyar ko mambobinta na shirin kai hari, yana mai jaddada cewa kungiyar ba ta taɓa aikata tashin hankali ba.
Ya ce:
“Tun daga kafuwar Islamic Movement a Najeriya kusan a shekarar 1977, ba mu taɓa kai wa kowa hari ba, kuma ba mu taɓa bayar da umarnin kai hari kan kowa ba.
“Ba mu taɓa kai hari ba kuma ba za mu taɓa kai hari ba. Ba haka tsarinmu yake ba, ba haka aka gina mu ba, kuma addininmu ba ya koyar da kai hari kan kowa.”

Source: Facebook
'Yan Shi'a sun kalubalanci Amurka
Ya kuma yi tambaya kan dalilin da ya sa ofishin jakadancin Amurka ya fitar da gargadi ga jama’a maimakon ya kai korafinsa ga hukumomin tsaron Najeriya.
“Me ya sa ofishin jakadancin zai fito fili ya sanar da jama’a haka? Idan akwai wata barazana, abin da ya dace shi ne a kai rahoto ga ‘yan sandan Najeriya domin su bincika kuma su kamo masu shirya hakan,”
Inji shi.
Iran: An kama dan Arewa a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Amnesty International ta yi zargin cewa an kama wani matashi bisa zargin wallafa sakonni kan yaki da ake a Gabas ta Tsakiya.
Amnesty ta kara da cewa tun bayan kama matashin a ranar Juma'ar da ta wuce bai samu damar ganawa da lauyoyinsa ba ko kuma iyalansa.
Kungiyar ta yi kira ga hukumar DSS da ta sake shi nan take ko kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu idan har ya karya dokar kasar nan.
Asali: Legit.ng
