Aminu Ado Bayero Ya Shirya Hawan Sallah a Kano, ba a Ji Labarin Sanusi II ba
- Mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero ya fara shirye-shiryen hawan sallah yayin da azumin watan Ramadan 2026 ke kokarin karewa
- Sarkin ya tura takarda ga rundunar 'yan sandan jihar Kano yana sanar da ita jadawalin ayyukan da ya tsara game shagalin hawan sallah
- Tun bayan sauke Sarki Aminu Ado Bayero da dawo da mai martaba Muhammadu Sanusi II 'yan sanda ke hana hawan sallah a Kano
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Alamu sun nuna cewa za a sha kallo a jihar Kano kasancewar mai martaba Aminu Ado Bayero ya fara shirye-shiryen hawan sallah.
Shirye-shiryen hawan sallar da Aminu Ado ya tsara sun dauki hankali ne kasancewar Sarki Muhammadu Sanusi ma zai iya shirya hawan sallah a jihar.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da masarautar Kano bangaren Aminu Ado ta fitar ne a wata wasika da fadar shi ta wallafa a shafinta na X.
Aminu Ado na shirin hawan sallah
Fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ta sanar da rundunar ‘yan sandan Najeriya a Kano a hukumance kan shirye-shiryen gudanar da bukukuwan sallah.
A wata wasika mai dauke da kwanan wata 7 ga Maris, 2026, wadda aka aike wa kwamishinan ‘yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori, majalisar masarautar ta ce za a gudanar da bukukuwan sallah ne daga fadar sarki da ke Nasarawa a Kano.
Sanarwar da Abdullahi Haruna Kwaru, ya sanya wa hannu, ta ce sarkin tare da mambobin Majalisar Masarautar Kano sun amince da jadawalin ayyukan da za a gudanar.
Bukukuwan da Aminu Ado zai yi
A cewar wasikar, bukukuwan Sallah da aka amince da su za su kunshi jerin gwanon Durbar da suka hada da Hawan Sallah, Hawan Daushe, Hawan Nasarawa da Hawan Panisau, tare da sauran wasannin al’adu.
Fadar ta ce cikakkun bayanai na shirin, da suka hada da ranaku, lokuta da wuraren da za a gudanar da jerin gwanon, suna kunshe cikin wani jadawali da aka hada tare da wasikar da aka tura wa hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan
"Kada a dagula siyasar Kano": NNPP ta aika sako kan shirin tsige Mataimakin gwamna
Zuwa lokacin hada wannan rahoton, Legit ta bibiyi shaukan sada zumunta na mai martaba Muhammadu Sanusi II ba tare da ganin wata sanarwa game da bukukuwan sallah ba.
Aminu Ado ya godewa 'yan sanda
Daily Trust ta rahoto cewa sarkin da mambobin majalisar masarautar sun yi godiya saboda hadin kan da hukumomin tsaro ke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsari a jihar Kano.
Bayan kammala bayanai game da hawan sallah, fadar ta kuma yi addu’ar a gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da nasara a fadin jihar.

Source: Twitter
A baya dai ‘yan sanda sun haramta hawan sakamakon rikice-rikicen da suka biyo bayan takaddama tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II.
Tinubu ya ba Aminu Ado mukami
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba mai martaba Aminu Ado Bayero mukamin da ya shafi yankunan Najeriya.
A bisa sanarwar da Legit Hausa ta samu, Aminu Ado yana jagorantar kwamitin ciyar da mutane a Ramadan a yankunan kasar nan.
Mai martaba Aminu Ado Bayero ya yi godiya ga shugaban kasa tare da jaddada cewa zai yi aiki tare da 'yan kwamitin domin samun nasarar aikin.
Asali: Legit.ng
