Za a Yi Amfani da Dakarun Sojojin Sama a Zaben 2027 a Najeriya

Za a Yi Amfani da Dakarun Sojojin Sama a Zaben 2027 a Najeriya

  • Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) na shirin amfani da jirage da fasahar leƙen asiri domin tallafa wa a zaɓen 2027
  • Shugaban Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ya bayyana hakan yayin ziyarar girmamawa ga hukumar INEC
  • INEC ta ce za ta kafa ƙungiyar aiki ta haɗin gwiwa da NAF domin shirya harkokin tsaro da sufuri kafin zaɓukan gaba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta bayyana cewa tana ɗaukar matakan da suka dace domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro a zaben 2027.

Daga cikin ayyukan da rundunar za ta taimaka da su akwai jigilar kayayyakin zaɓe gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

INEC na shirin aiki da rundunar soji kafin 2027
Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Shugaban Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, ne ya bayyana hakan lokacin da ya kai ziyarar girmamawa hedikwatar hukumar INEC a Abuja.

Kara karanta wannan

Najeriya ta kai wa mutanenta da suka makale a yaƙin ƙasar Iran agaji

Sojojin sama za su yi aiki da INEC

Tribune Online ta rahoto Air Marshal Sunday Kelvin Aneke ya ce rundunar na tsara yadda za ta yi amfani da jiragen sama da take da su domin taimakawa INEC.

Za a yi amfani da su wajen jigilar kayayyakin zaɓe da ma’aikatan da za su gudanar da aikin zaɓe zuwa sassa daban-daban na ƙasar.

Aneke ya bayyana cewa wasu daga cikin manyan jiragen rundunar masu ɗaukar kaya, musamman jiragen C-130, a halin yanzu suna wajen ƙasar domin yin gyaran da aka tsara tun da wuri.

Sai dai duk da haka, ya jaddada cewa rundunar ba za ta gaza ba wajen samar da wasu jirage da za su iya maye gurbin waɗanda ake gyara wa domin tabbatar da cewa an kai kayan zaɓe da ma’aikata a kan lokaci.

INEC ta ce an shirya domin tabbatar da sahihin zabe
Shugaban INEC Joash Amupitan tare da wasu manyan jami'an INEC mata biyu Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Ya ce:

“Duk da cewa ana gyaran wasu jiragenmu a waje, muna shirye-shirye domin amfani da sauran jiragen da muke da su don taimakawa wajen kai kayan zaɓe da ma’aikata cikin gaggawa.”

Kara karanta wannan

ICPC: Lauyan El Rufa'i ya yi martani kan 'gano' gidajen tsohon gwamna a kasar Masar

INEC ta yi maraba da taimakon sojojin sama

A nasa jawabin, shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar za ta kafa wata ƙungiyar aiki ta musamman da NAF gabanin zaben.

Ya ce ziyarar da Shugaban Sojin Sama ya kai hedikwatar INEC wata alama ce ta tabbatar da cewa rundunar soji a shirye take ta ba da goyon baya ga tsarin zaɓe a ƙasar.

Amupitan ya ƙara da cewa rundunar na kuma shirya amfani da fasahar ISR domin ƙara sa ido a lokacin zaɓe, domin gano duk wata barazana ta tsaro tun kafin ta taso.

A cewarsa, irin wannan fasaha za ta taimaka wajen gano matsaloli da wuri, tare da bai wa hukumomin tsaro damar ɗaukar matakan gaggawa domin kare lafiyar jama'a.

Hukumar INEC ta magantu a kan zabukan 2027

A baya kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ta ce ba za ta iya ba da tabbacin cikakken zaɓe mai nagarta 100% a 2027 ba yayin da yan Najeriya ke fatan sahihin zabe.

Kara karanta wannan

ICPC ta gano wasu gidajen alfarma da ake zargin El Rufai ya mallaka a ƙasar waje

Shugaban hukumar, Joash Amupitan ya ce zaɓen 2027 zai fi kowanne a tarihin Najeriya saboda shirin da aka yi masa domin tabbatar da cewa an samu zabe da kowa zai amfana.

Hukumar ta ce tana ƙoƙarin inganta jigilar sakamakon zaben da sauran harkokin kayan aikin zabe yayin da ya saura watanni a kaɗa kuri'a a sabuwar shekara mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng