Iran: An Kama Dan Arewa kan Magana game da Yakin Amurka da Isra'ila
- Kama wani matashi mai suna Sani Waspapping a jihar Kaduna da aka ce hukumar DSS ta yi ya tayar da kura a kafafen sada zumunta
- Kungiyar Amnesty International mai rajin kare hakkin dan Adam ta bayyana cewa ana zargin kama Sani ne kan yakin da ake a Gabas ta Tsakiya
- Wasu rahotanni sun bayyana cewa Sani Waspapping ya kasance daya daga cikin masu nuna goyon baya ga Iran tare da caccakar Amurka
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Amnesty ta yi Allah-wadai da tsare wani mai tasiri a shafukan sada zumunta a Kaduna kan sakonninsa game da yakin Amurka da Isra’ila da Iran
Amnesty ta yi Allah-wadai da zargin tsare Sani Waspapping da aka ce hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta yi, inda ta bukaci hukumomin Najeriya su gurfanar da shi a gaban kotu ko kuma su sake shi nan take.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Amnesty ta yi ne a cikin wani sako da kungiyar ta wallafa a shafinta na Facebook.
Yadda aka kama mai sukar Amurka
A wata sanarwa da Amnesty ta fitar, kungiyar ta ce an kama Waspapping a Kaduna ranar Juma’a kuma har yanzu yana tsare ba tare da samun damar ganin iyalansa ko lauyoyinsa ba.
Kungiyar ta ce yanayin da aka kama shi a ciki ya tayar da hankali matuka kan yadda ake gaza girmama dokokin kasa da kuma da kare hakkokin bil’adama a Najeriya.
A cewar Amnesty, ana kyautata zaton cewa an kama Waspapping ne saboda wasu sakonni da ya wallafa a shafukan sada zumunta dangane da yakin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ta ce:
“An kama Sani Waspapping a Kaduna ranar Juma’a kuma har yanzu yana tsare ba tare da samun damar ganin iyalansa ko lauyoyinsa ba.”
An kama wani kafin Sani Waspapping
Kungiyar ta kara da cewa Waspapping shi ne mutum na biyu da aka ruwaito cewa SSS ta tsare dangane da martanin da mutane suka nuna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.
Amnesty International ta bukaci hukumomin Najeriya su tabbatar da cewa an girmama hakkokinsa tare da bin dukkan matakan doka yadda ta kamata.
Daily Nigerian ta rahoto kungiyar ta ce:
“Dole hukumomin Najeriya su mutunta dokokin kasa a kowane lokaci — ciki har da a lamarin Sani Waspapping.”
Kungiyar ta kuma bukaci a ba wanda ake tsare din damar ganin iyalansa cikin gaggawa tare da samun cikakken taimakon lauyoyinsa.

Source: Getty Images
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumar SSS ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan kama Sani Waspapping.
Koriya ta Arewa ta goyi bayan Iran
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Koriya ta Arewa ta nuna goyon baya ga Iran bayan zaben sabon jagoran addini, Mojtaba Khamenei.
Ta bayyana cewa ta mutunta ra'ayin Iran wajen zaben wanda zai maye gurbin Ayatollah Ali Khamenei da Amurka da Isra'ila suka kashe.
Koriya ta Arewa ta caccaki shugabannin Amurka da Isra'ila game da harin da suka kai, inda ta ce hakan ya saba dokokin kasa da kasa.
Asali: Legit.ng


